Ra'ayi: Farfadowar Tattalin Arzikin Najeriya
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi: Farfadowar Tattalin Arzikin Najeriya

Hukumar Kiddiga ta kasa a Najeriya ta ce tattalin arzikin kasar ya fita daga tabarbarewar da ya kwashe sama da shekara guda yana ta yi, har ma ya fara marowa. Arzikin da kasar take samu daga abubuwan da take samarwa ya karu da abin da ya kai kashi uku da digo ashirin da uku a cikin dari a rubu'in shekara da ya wuce. Ko ya kuke kallon wannan sanarwa? Batun da muka tattauna da shi kenan a filin Ra'ayi Riga na wannan makon.