Adikon Zamani
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Me ke jawo sabani tsakanin ma'aurata?

  • Akwai cikakkiyar tattaunawar da Fatima Zarah Umar ta yigame da matsalar cin zarafin mata, sai ku latsa alamar lasifika da ke sama don sauraro.

Najeriya ta na daya daga cikin kasashen da ake yawan samun cin zarafin mata a yankin kudu da hamadar Saharar Afirka, inda biyu bisa uku na matan ke fuskantar cin zarafi daga takwarorinsu maza, kamar yadda kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce.

Kamar yadda yake a sauran kasashen Afirka, matsalar cin zarafin mata abu ne da ake yawan samu a cikin al'umma.

Galibin mata suna mika wuyansu ne ga mazajensu, su na taimaka musu wajen zamantakewar rayuwa.

Amma kuma sai ka ga a wasu lokuta mazajen su na musguna wa matan da kuma duka a wani yunkuri na nuna ikon da aka san su da shi a al'adance.

Akwai wadansu al'ummomi da suka lamunci dukar mata kuma hakan ya zama kamar al'ada ce a doke mace.

Wani nazari da wadansu manazarta biyu Oyediran da kuma Isiugo-Abanihe suka yi a shekarar 2005, ya gano cewa mata da kansu sun fara lamuntar duka a mtsayin wata hanya da maza suke ladaftar da su idan sun aikata ba daidai ba.

A arewacin Najeriya, yi wa mace tsawa da zagi da kuma duka wadansu abubuwa ne da ake yi idan ana so a gyara tarbiyyar macen da aikata ba daidai ba.

Amincewa da hakan daga bangaren al'umma shi ne ya sa wadansu mazajen suke ci gaba da ji wa mata rauni da kuma cusa masu bakin ciki a zuciya, bisa tunanin su ne suke da alhakin ladaftar da matansu.

Akwai lokutan da wasu suke kafa hujja da hadisa kan "duka ko tsangwamar matan da suka aikata ba daidai ba."

Na tambayi Shugabar Bangaren Mata na Hukumar Hisba a jihar Kano Dokta Fatima Zahra Umar kan sahihancin hadisin kuma ta yi mini karin bayani kamar haka.

Manzon Allah (SAW) bai ce maza su doke matansu ba, ya bukaci da su kaurace musu wajen kwanciya ne, wanda hakan ya fi yi wa mata ciwo, a cewar Dokta Fatima.

A al'adance laifin mace ne idan mijinta ya doke ta, ko ya wulakanta ta.

Sai ka ga mace ta rasa wurin da za ta kai kokenta yayin da mijinta ya doke ta.

Idan mijinki ya doke ki, to kila saboda ba ki jin magana ne, ko kuma ba ki daraja shi, ko kuma ba ki fahimci shi ba ne... haka za kai ta ji.

Da wuya ka ji wata magana mai kyau, ko ka ga an dauki wani mataki a kan mijin. To me ya sa haka?

Me ya sa muke yi wa masu dukan matansu uzuri? Me ya sa al'ummar da muke ciki take saurin dora wa matan laifi, amma ba miji ba?

Akwai lokacin da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu ya ce ya ba 'ya'yansa mata umarnin idan mijinsu ya doke su, su rama.