Kwalara ta hallaka mutum 528 a Congo

Cutar kwalara na kara kamari a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cutar kwalara na kara kamari a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo

Hukumar lafiya ta duniya (WHO), ta ce, barkewar cutar amai da gudawa wato kwalara da aka samu a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, ta zamo abin damu wa matuka.

Akalla mutum 528 a kasar sun rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar a wannan shekarar ya zuwa yanzu.

Hukumar lafiyar ta ce, akwai wadanda suka kamu da cutar fiye da dubu 34 a kasar.

A cewar hukumar, an samu bullar cutar ta kwalara a larduna 20 daga cikin larduna 26 da kasar ke da su, sannan cutar kuma ta bulla har zuwa manyan biranen kasar ciki har da Kinshasa.

Hukumar lafiyar ta ce, tun daga watan Yunin da ya gabata, ana samun mutum 1,500 na kamuwa da cutar a duk mako a kasar.

Wani bincike da hukumar ta gudanar a kasar ya nuna cewa, an fi kamuwa da cutar kwalarar a yankin Kasai, inda sha'anin tsafta da tsaro ke da rauni.

A shekarar 2016, cutar kwalarar, ta hallaka mutum 817 a kasar ta Congo.

Labarai masu alaka