An kara wa'adin shiga gasar Hikayata ta 2017 ta cin $2000

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Bayanin Jimeh Saleh kan kara wa'adin karbar labarai a gasar Hikayata

Shin ina mata iyayen giji? Sashen Hausa na BBC ya sake bude gasar rubuta ƙagaggun labarai ta mata zalla a karo na biyu.

Gasar Hikayata, wani kokari ne na bai wa mata damar fito irin basirar da Allah ya hore musu wajen rubutu da kirkirar labari.

Ga masu sha'awar shiga gasar sai su rubuta ƙagaggen labari wanda bai fi tsawon kalma 1,000 zuwa 1,500 ba, daga ranar Talata, 15 ga watan Agusta, 2017.

Ana iya aiko da rubutun ta hanyar imel na Labari.bbchausa@bbc.co.uk har zuwa ranar Asabar 30 ga watan Satumba da za a rufe gasar.

A ranar 1 ga watan Agustan 2016 ne Sashen Hausa na BBC ya fara karbar kagaggun labarai a wannan gasa ta mata zalla karon farko a tarihi.

Za a iya karanta ka'idojin shiga gasar a nan.

Image caption Hikayata gasa ce ta rubutu don mata kawai

Wannan gasa tana da burin taimakawa wajen bunkasa rubutu a tsakanin mata da rage gibin da ke tsakaninsu da maza, wanda rashin daidaito ta fuskar samar da ilimi ya haifar.

A karon farko na gasar Hikayata, Aisha Muhammad Sabitu ce ta zama gwarzuwa, inda aka ba ta lambar yabo da kuma $500.

Aisha, wadda ta fito daga jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, ta rubuta kagaggen labari mai suna "Sansanin 'Yan Gudun Hijira".

Sai kuma, Amina Hassan Abdulsalam ta zo ta biyu, da labarinta mai suna "Sai Yaushe?", yayin da Amina Gambo ta zo ta uku da labarin "In Da Rai".

Image caption Aisha Sabitu ce gwarzuwar gasar Hikayata a karon farko a bara
Image caption Karo na biyu kenan da BBC Hausa take bude gasar Hikayata saboda mata zalla