Me kyautar da Saudiyya ta yi wa Trump ke nufi?

President Donald Trump receives the Order of Abdulaziz al-Saud medal from Saudi Arabia's King Salman bin Abdulaziz al-Saud at the Saudi Royal Court in Riyadh. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Abdulaziz al-Saud na saka wa Trump kyautar sarka

A lokacin da Winston Churchill ya kai wa Sarki Abdul Aziz ibn Saud ziyara a watan Fabrairun 1945, ba jimawa ya gano turaren da ya kawo na dala 134 bai dace da alkyabbar ba, da takobi ,da wuka da kuma zobunan zinare da ya karba a komawarsa.

Duk da guguwar Yakin Duniya na Biyu, Firaiministan Birtaniya ya koma gida kuma ba tare da ba ta lokaci ba ya umarci daya daga cikin kamfanin kera motoci su kera mota a kai wa sarkin bayan wata bakwai.

A yau shugabannin duniya ba sa iya yin kyautar jirage ko motoci masu tsada, amma wasu kasashe na baya-bayan nan sun ba wa shugaba Donald Trump kyautar abubuwa 83 a lokacin da ya kai ziyara kasar Saudiyya, wanda ake daukarta a matsayin fariya a daular Larabawa.

Wacce kyauta Trump ya karba?

A lokacin da Shugaba Trump ya kai ziyara kasashen waje a karon farko, ya halarcin taron kasashen Larabawa da aka yi a babban birnin Saudiyya Riyadh, inda Sarki Salman ya ba shi manyan kyaututtuka da suka hada da takobi, da wukake, da gwala-gwalai, da gomman harami, da sauran tufafin Larabawa na gargajiya, da takalman fata da kuma turare.

Sai dai kuma kyaututtukan ba wasu na alfarma ba ne, in ji Ali Shihabi, daraktan gidauniyar Larabawa.

Mista Shihabi ya ce, "A shekarun baya gwamnatin kasashen Larabawa na bayar da kyautar fariya, inda suke bayar da agoguna masu tsada, da sarkoki da makamantansu.

Yanzu kuwa suna bayar da kyautukan ne na kayayyakin gargajiya, in ji shi.

Ellen Wald, wani dan Amurka kwararre a gabas ta tsakiya kuma marubuci, ya ce, a zahiri kyaututtukan na gargajiya ne, kuma ya nuna irin tafiyar da kuma mutanen da suka shiga tawagar rakiyar Trump zuwa Riyadh.

Mambobin wakilan Amurka da suka ziyarci Saudiyya a shekarar 2008, sun karbi irin wadannan kyaututtuka da suka hada da wukake, da sarkoki, da kuma rigunan sarauta, in ji ta.

Ko zai iya adana su?

Dokokin kasar Amurka ta haramta wa ma'aikatan gwamnati karbar duk wata kyauta daga gwamnatin wata kasar da ta kai kimar abin da ya fi dala 390.

An samo wannan dadaddiyar dokar ne tun shekarar 1966, wacce ta haramta karbar kyautar fiye da "abin da ya wuce kima", don hana gwamnati hangen karbar wani abu daga diflomasiyyar Amurka da kyautar dawakai, da motocin alfarma wata kila ma kirar Rolls-Royc ko biyu.

A shekarar 1978, dokar ta bayyana cewa, mafi karancin kyautar dala 100, sakamakon hauhawan farashi da ake samu ake karawa duk bayan shekara uku.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An haramta wa ma'aikatan gwamnatin Amurka karbar kyautar abin da kimarsa ya wuce Dala 390 daga kasashen ketare

Kyautuka na baya da aka ba wa shugabannin Amurka da sauran shugabannin diflomasiyya ana ajiye su ne a gidan adana kayan tarihi, ko a dakin karatu na fadar shugaban kasa, ko kuma a yi gwanjon su.

Har'ila yau ana ba wa jami'an gwamnati zabin su sayi kyautar da suka karbo a kan farashin kasuwa.

Tsohuwar sakatariyar harkokin wajen kasar Hillary Clinton ta yi amfani da irin wannan zabin a shekarar 2012, a lokacin da ta sayi wata sarka da jagorar 'yan adawa kasar Myanmar Aung San Suu Kyi ta ba ta. Inda aka yi wa sarkar kudin da ya kai dala 970.

Ko wannan abu ne da aka saba gani?

Ziyarar shugabannin kasashe suka kawo musayar ra'ayi, wasu lokutan kuma a akan kyautukan ne.

Daraktan harkokin kasashen Larabawa na ma'aikatar Gabas ta Tsakiya, Gerald Feierstein ya ce, kyautar da ake bayar wa ba bakon abu ba ne a daular Larabawa.

Ya kara da cewa, ya tuna kyautar agogon da gwamnatin Bahrain ta ba shi, lokacin da suka kai ziyara yankin Gabas ta Tsakiya a shekarar 1990, a lokacin yana mataimakin darakta a ofishin harkokin yankin Larabawa da ke shiyyar kasar.

"Kamar irin wani abu ne da ba za a iya ba ni ba, kawai sun bayar da wadannan agogunan ne ga dukkan mambobin wakilan," in ji shi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta taba bukatar gwamnatoci kasashen ketare da su daina bai wa Shugaba Bill Clinton kyautar sarewa

A lokacin da zai mika agogon mai tsada ga hukumar kula da harkokin waje, wacce take aikin adana kyautar diflomasiyya, ya shaida musu cewa, akwai "Dakin da yake cike da agoguna daga Bahrain".

Mista Feierstein ya tuna lokacin da ma'aikatar harkokin waje ta hana gwamnatin wata kasa ba wa shugaba Ronald Reagan kyautar dawakai.

A shekarar 2015 ne, Barack Obama ya karbi wasu kayayyaki da suka hada da zanen hotunan wasu maza da suke kwallon kwando daga Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da kuma kwanon zinare na dala 110,000 daga Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, da kuma fiyano na kida daga Sarki Salman.

Mista Obama ya yi matukar mamaki a lokacin da ya ba wa Firai ministan Birtaniya Gordon Brown wani akwati mai dauke da faifain bidiyon fina-finan Amurka, wanda mutane da dama suke kallonsa a matsayin cin mutunci ga shugaban Birtaniya.

Ko jerin kyautar da aka yi wa Trump na nufin wani abu?

Misis Wald ta ce, "Trump ya soki abokiyar hamayyarsa ta jam'iyyar Democrat Hillary Clinton , a kan karbar kyauta daga Saudiyya wacce kuma ta jawo surutai da karin gishiri game da gwamnatin, tana yiyuwa kyaututtukan da ya karba ba za ta karfafa alakarshi da kasar ba".

Ta yi bayanin cewa, "hakan ya nuna wata al'adar yankin ne fiye da kowacce alamar diflomasiyya ko wata dangantaka."

Ta kara da cewa, bakon abu shi ne yadda Trump ya kai ziyara kasar ta wasu kwanaki, saboda an saba ganin haka ne kafin fara amfani da jirgin sama.

Jakadan Amurka na farko a Saudiyya , J Rives Childs, ya kan yi tafiyar kwana uku idan zai je kasar Saudiyya, lokacin da zai karbi wasu kayayyaki da suka hada da takobin zinare, da agogo da kuma wukar zinare.

Misis Wald ya kara da cewa, a wani taro da aka yi ya ki amincewa da damar yin kwarkwara a Riyadh.

"Aikin gwamnati ne mara wa masana'antun kasar baya ta hanyar yi wa shugaban Amurka kyauta da wasu kayayyaki," in ji Mista Shihabi.

"Bayar da kyautuka na nuna karramawa da kuma karbar baki," in ji shi.

Labarai masu alaka