Yadda wasu nakasassu suka dawo daga rakiyar bara a Nigeria

Wadansu daga cikin kayayyakin da guragun suka kera
Image caption Wadansu daga cikin kayayyakin da guragun suka kera

Wasu nakasassu a jihar Kaduna a arewacin Najeriya sun yi watsi da bara, inda suka rungumi sana'o'in hannu.

Gwamnatin Najeriya ta kwashe tsawon lokaci tana bukatar wayar da kan nakasassu a kan su daina bara.

Nakasassun sun ce sun yi watsi da bara ne saboda matsalolin rayuwar da suka shiga a dalilin yin barar.

Saboda haka ne suka ce sun ga ya dace su koma su nemi sana'ar hannu don dogaro da kai.

Nakasassun sun shaida wa BBC cewa, akwai sana'o'i da dama da za su iya yi kamar kere-kere da aikin kafinta da walda da dai sauransu.

Daya daga cikin nakasassun ya ce bara ba sana'a ba ce, face zubar da mutunci da kaskanci, don haka yake kira ga sauran 'yan uwansu nakasassu a ko ina a Najeriya, da su ma su ajiye bara, su kama sana'a.

Image caption Wadansu kujerun makaranta da guragun suka yi

Mabaratan da suka jingine barar sun shaida wa BBC cewa, bayan sun yanke shawarar daukar wannan mataki, sun samu horo daga hukumar sauya tunanin mabarata wato Rehabilitation Board ta jihar, inda aka koya musu sana'o'i daban-daban.

Kuma a cewarsu a yanzu kwalliya ta fara biyan kudin sabulu, tun da a yanzu sana'a na samar musu abin rufin asiri.

Yawanci babbar matsalar da matasa wadanda suka daina bara ke fuskanta ita ce ta rashin jari, wanda hakan ya sa suke ganin ya kamata gwamnati ta yunkura domin taimaka musu da jari.

A kasar dai, a yanzu akwai bankuna da hukumomin da ke ikirarin bayar da basuka ga masu son kafa sana'o'i, to amma akasari akan sha wuya kafin a samu irin wannan bashi.

Labarai masu alaka