Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka a makon jiya 15-21 ga Satumba 2017

Wasu daga cikin kyawawan hotuna daga ko'ina cikin nahiyar Afirka da kuma na 'yan Afirka dake zaune a wasu sassan duniya a makon da ya gabata.

Hakkin mallakar hoto AFP

Daniel Laruelle kenan dan Afirka ta kudu a lokacin gasar hawan igiya da aka gudanar a kasar Switzerland ranar Juma'a. Mutum na biyar da ke da kwarewar wasan a fadin duniya, yayin da yake tafiya a kan igiyar da ke da tsawon mita 45 zuwa 304.

Hakkin mallakar hoto Reuters

A rana ta biyu kenan, wannan wani magoyin bayan kungiyar kasar ta afirka ta kudu, ya bayyana da matukar shaukin wasan duk kuwa da rashin nasara da kasar tasa ta yi a hannun mai masaukin baki, ranar Asabar.

Hakkin mallakar hoto PA

A ranar Alhamis ne masu hako ma'adinai a Uganda suke neman zinare, bayan da gidauniyar Fairtrade Foundation ta bayar da sanarwar hako Zinare karon farko a kasar.

Hakkin mallakar hoto EPA

A ranar Asabar ne wani da ya kai ziyara kabarin Maya a Giza da ke Masar, ya yi sha'awar tsofaffin kayan mutanen da, kabarin na yankin makabartar Saqqara, wacce ake tunanin ta samo asalin tun shekaran aru-aru da suka shude.

Hakkin mallakar hoto AFP

'Yan kasar Habasha kenan Zayd Hailu ke fafatawa a gasar tseren kekuna ta duniya da aka gudanar a kasar Norway ranar Talata, a wannan lokacin ne kuma aka sace mata keken nata. 'yar wasan mai shekara 17 ta ce kudin keken nata ya kai albashinta na shekara uku. Ta yi matukar damuwa a rana ta biyu da sace mata keken.

Hakkin mallakar hoto EPA

A ranar Lahadi, magoya bayan dan takarar jam'iyyar adawa a kasar Kenya Raila Odinga ke ihu yayin da ya ke yi musu jawabi a lokacin gangamin yakin neman zabe a birnin Nairobi.

Duk da samun nasar da ya yi a gaban kotun kasar kan batun soke zaben sakamakon kurakurai da aka samu a sakamakon zaben, Mista Odinga ya ce shi da jam'iyyarsa ba za su shiga zaben zagaye na biyun ba, har sai hukumar zaben kasar ta yi wa ma'aikatanta garambawul.

Hakkin mallakar hoto AFP

A rana ta biyu kuma wani mutum ya yi wa rakumarsa mai suna Junoir kwalliya da alamar jam'iyya mai mulki ta Jubilee Party a wani yunkuri na nuna goyon bayansa ga jam'iyyar.

Bayan da aka yi ta shakku game da kayyakin da za a guidanar da zaben a ranar 17 ga watan Oktobar, sai dai daga baya an jinkirta ranar zaben da kwanaki tara.

Hakkin mallakar hoto AFP

A ranar Talata ne aka dauki hoton wadannan masu zanga-zanga kuma suna cikin dubban mutanen Togo da suka fito kan tituna a makonnin da suka gabata, inda suke bukatar sauka kundin tsarin mulkin kasar da kuma kira da shugaban kasar Faure Gnassingbé ya yi murabus.

Hakkin mallakar hoto Reuters

A ranar Juma'a ne wani ya rungume jaririnsa bayan da masu aikin ceto masu zaman kansu suka ceto su, a lokacin da ake aikin ceton 'yan ci ranin gabar tekun Libya.

Labarai masu alaka

Labaran BBC