Nigeria: An kori jami'an Kwastam 'kan shigo da makamai'

Wadannan su ne bindigogin da hukumar kwastam ta kama cikin wannan makon
Image caption Wadannan su ne bindigogin da hukumar kwastam ta kama cikin wannan makon

Masana harkokin tsaro sun fara tofa albarkar baki musammam game da jami'an hukumar kwastam 28 da ake zargi, da hannu wajen kawar da kai ga makaman da ake satar shiga da su Najeriya.

Babban kwanturolan hukumar, Kanal Hamid Ali ya ce bayan kammala bincike da hukumar tasa ke da alhakin yi kan lamarin, ta mika makaman da wadanda ake tuhuma ga hukumar tsaro ta farin kaya ta kasar, kuma tuni an mika su ga kotu don a yi musu hukuncin da ya dace.

"Mu kuma namu jami'an da muka kama su da hannu a ciki tuni muka kore su daga aiki."

A baya-bayan nan dai hukumar kwastam ta Nigeria ta kama bindigogi 470 a tashar jiragen ruwan Tincan Island a Lagos, wadanda aka shigo da su daga kasar Turkiyya, makonni kadan da shigo da kama wasu fiye da 1,000 da suma aka shigo dasu daga Turkiyyan.

Gwamnatin kasar ta ce dole ta hau teburin tattaunawa da ofishin jakadancin Turkiyya da ke kasar.

Malam Kabir Adamu, wani mai sharhi ne kan harkokin tsaro, ya kuma shaida wa BBC cewa duk da yake babu cikakkiyar shaida mai alakanta irin wannan sakaci na jami'an kwastam, da shigar irin wadannan makamai hannun kungiyoyi irinsu Boko Haram, da masu satar mutane da kuma sauran masu gwagwarmaya da makamai, ana iya cewa al'amarin ba karamar barazana ba ce ga Najeriya.

Ku latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron cikakken bayanin da Malam Kabir ya yi wa abokin aikinmu Usman Minjibir:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Bayanin Kabir Adamu kan hukumar kwastam

Labarai masu alaka