An gano dalibi bayan kwana uku ba ci ba sha

Dance party Hakkin mallakar hoto Getty Images

An ceto wani dalibi a jihar Indiana ta Amurka bayan takwarorinsa sun bar shi a baya inda ya shafe kusan kwana uku cur a cikin wani kogon da suke zuwa raye-raye.

Bayan rabuwar Lukas Cavar da ayarin abokansa, sai ya iske kofar kogon garkame da kwado.

Layin sadarwa ya yi kasa a wayarsa ta salula, kuma duk ihun neman dauki da ya yi tsawon sa'o'i bai iya kai wa ga kunnen wani mahaluki ba.

Lukas Cavar ya ce ya rayu ne ta hanyar tsotsar danshin da ke jikin ganuwar kogon tare da zuba wa kansa surutu.

Daga baya ne aka gano shi a kusa da kofar kogon yana sharar barci.

Ba a san yadda aka yi har ya rabu da abokan tafiyarsa ba.