Kotu ta ba Ghana gaskiya a shari'a da Ivory Coast

Ghana Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ma'aikatar hakkan mai ta Ghana

Wata kotun kasa da kasa ta yanke hukuncin cewa Ghana ba ta keta 'yancin Ivory Coast ba, sakamakon aikin hakkan mai da take gudanarwa a tekun da a ke takaddama akai.

Shekaru uku kenan da Ghana ta kai batun ga kotun kasa da kasa dake shari'a kan takaddama a teku, bayan Ivory Coast ta zarge ta hakkan mai a cikin ruwa da yake mallakinta.

Ghana ta ce ta shafe shekara da shekaru tana aiki a yankin, kafin Ivory Coast ta yi ikirarin mallakin shi.

Duk da cewa Ghana ta na da dumbun arzikin mai a cikin teku, faduwar farashin mai a kasuwannin duniya ta sa kudaden shigar kasar ya ragu sosai.