Jiragen yakin Amurka sun yi shawagi a kusa da Koriya ta Arewa

America Hakkin mallakar hoto US PACIFIC COMMAND
Image caption Irin jiragen yakin Amurka da suka yi shawagi a kusa da Koriya ta Arewa

Rundunar sojin saman Amurka ta tura wasu jiragen yakinta masu lugudan bama-bamai yin shawagi a sararin samaniyar tekun dake gabashin Koriya ta Arewa.

Ma'aikatar tsaro Pentagon ta ce wannan ne karon farko a karni na ashirin da daya, da jiragen yakin Amurkan suka yi nisan zango kusa da Koriya ta Arewar.

Wani mai magana da yawun rundunar sojin saman ta Amurka, ya ce an tura jiragen ne domin a nuna da gaske Amurka take ta yi maganin rashin kan gadon Koriya ta Arewa.

Jim kadan bayan jiragen sun yi shawagi, ministan harkokin wajen Koriya ta Arewa, a jawabin da yayi wa majalisar dinkin duniya, ya kare matakin kasar shi na kera makaman nukiliya.