An dabawa likita wuka a kan hanyarsa ta zuwa masallaci a London

Altrincham and Hale Muslim Association Hakkin mallakar hoto Google Street View
Image caption An daba wa Dokta Nasser Kurdy wuka ne a kan hanyarsa ta zuwa masallataci

An daba wa wani likita wuka a bayan wuyansa lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa masallaci a yankin Greater Manchester a kasar Ingila, wani al'amari da ake zargin nuna kiyayya ne.

An kai wa Likita Nasser Kurdy, wanda babba ne a bangaren tiyata, harin ne a wajen wata cibiyar Musulunci ta Altrincham and Hale, da misalin karfe 17:50 BST kuma an kai shi asibiti.

Tuni aka sallame shi daga asibiti, an kuma kama wasu mutane biyu masu shekaru 54 da 32 da ake tuhuma, ana musu tambayoyi.

'Yan sandan yakin Greater Manchester suna bukatar ganau su kawo shaidu.

Majiyoyi a yankin sun ce Kurdy ya ji wasu na kalaman kin jinin musulunci a yayin da aka kai masa harin.

'Yan sanda sun ce likitan mai shekara 58 shi ne mataimakin limamin masallacin yankin, kuma a ranar shi ne zai jagoranci sallah, a lokacin ne ya hango wani mutum a tsallaken hanya.

Jim kadan bayan haka ne, ya ji an daba masa wuka a wuyansa. Daga nan ne ya ruga a guje cikin masallacin, sannan ya kirawo masu bayar da agajin gaggawa.

Wani babban jami'in 'yan sanda, Russ Jackson ya ce wannan kazamin hari an kai shi ne ba tare da mutumin da aka kai wa, wanda mutane ke kauna, ya ce uffan ba.

''Kalaman Batanci''

Wani likita, Kalid Anis, mai magana da yawun masallacin, ya ce, ''Lamarin na iya fin haka muni .

Shi [Kurdy] ya ce ya lura da wani mutum a tsallaken hanya, sannan kuma sai kawai ya ji wani ya daba masa wuka ta bayansa.

''A lokacin da aka daba masa wukar, yana cikin gigita, don haka ba zan iya sanin irin kalaman da aka fada ba, amma na tabbata kalaman cin mutunci ne."

Akram Malik, limamin masallacin cibiyar Altrincham and Hale ya kara da cewa: '' Abin bakin cikin ne mutuka game da yadda aka kai hari kan wannan jagora a kan hanyarsa ta zuwa masallaci."

Labarai masu alaka

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba