Mata 100: Ko mata za su iya sauya duniya a mako daya?

President Sirleaf, Peggy Whison and Steph Houghton Hakkin mallakar hoto Getty Images

Masu iya magana na cewa rana ba ta karya, Allah Ya kawo mu shekara ta kawo mu.

Bana ma za mu kawo muku shirin mata 100 rabin muryar al'ummar duniya kamar yadda muka yi a kowace shekara.

Zuwa yanzu an bayyana sunayen mata 60 ciki har da matar da ta je sararin samaniyya, Peggy Whitson, da Shugaban Laberiya Ellen Johnson Sirleaf da kuma 'yar wasar kwallon kafar Ingila, Steph Houghton.

Za mu bayyana sunayen sauran guda 40 cikin watan gobe.

Jerin shirye-shiryen Mata 100 na shekara-shekara yana duba batutuwan da suke ciwa mata tuwo a karya ne - shin ko wannan shekarar za ta bai wa mata damar sauya al'amura.

Har ila yau cikin matan da za mu tattauna da su akwai mawakiya Rupi Kaur da Resham Khan (wadda aka watsa wa Acid) da kuma tauraruwar wani shirin talabijin, Jin Xing.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Jerin shirye-shirye za su kunshi labarai na cin zarafin da rashin adalci da sauransu, wadanda suke sanya gwiwoyin mata su yi sanni.

Saboda haka muna bukatar mata su yi tunanin hanyoyin magance wadansu daga cikin rashin adalcin da ake musu.

Bana ce shekara ta biyar da ake gudanar da wannan shiri na musamman kuma za a duba batutuwa hudu ne|:

1. Mata da suka cimma wani babban mataki

2. Ilimin Mata

3. Cin zarafin mata a bainar jama'a

4. Nuna wariya ga mata a fannin wasanni

Mene ne shirin Mata 100?

Shirin Mata 100 yana bayyana sunayen mata 100 wadanda suka yi zarra da tasiri a fadin duniya kowace shekara.

A shekarar 2017, muna bukatarsu da su magance wadansu manyan batuwa guda hudu da suke jawo wa mata cikas a yanzu - cimma wani babban mataki da batun ilimi da batun cin zarafi da kuma nuna wariya musamman a fannin wasanni.

Da taimakonmu, za su lalubo hanyoyin magance matsalolin kuma muna so su ba da gudunmuwa da shawarwari.

Za a iya tuntubar mu a shafukanmu na Facebook da Instagram da Twitter da kuma ta hanyar amfani da maudu'in #100Mata


Wadansu daga cikin mutanen da ke cikin jerin Mata 100 za su yi aiki ne daga birane hudu a tsawon mako hudu na watan Oktoban bana, inda za su samar da hanyoyin da za su taimaka wajen magance matsalolin.

Sauran za su ba da gudunmuwarsu daga sauran sassan duniya.

Za a bayyana ragowar sunayen mata 40, yayin da mata ke ci gaba da shiga shirin da kuma ba da gudunmuwarsu da kwarewarsu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Idan shirin Mata 100 ya yi nasara, an cimma hakan ne saboda mata daga sassan duniya sun taimaka wajen fahimtar wadannan matsaloli.

Saboda sun ba da gudunmuwarsu game abin da suka sani. Ko kuma sun zo da wani sabon abu da kansu.

Shirin Mata 100 zai tattauna da mata ta rediyo da intanet da kuma shafukan sada zumunta.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Batun mata da suka cimma wani babban mataki za a tattauna ne a birnin San Francisco, batun ilimin mata kuma za a tattauna shi ne a birnin Delhi, yayin biranen Landan da Nairobi za su waiwayi batun cin zarafin mata, birnin Rio kuma ya duba batun nuna wa mata wariya musamman a fannin wasannni.

Sai dai tattaunawar za a yi ta ne a duniya baki daya kuma muna so mu ji daga mata a ko ina suke a fadin duniya.

"A shekarar 2015, an tattauna batutuwa 150 a harsuna 10 daga kasahe 30, a shakarar 2016 an kara sunayen mata guda 450 a shafin rumbun bayanai na Wikipedia kuma a bana za mu duba batun damawa da mata," in ji editar shirin Mata 100 Fiona Crack.

"Zai kasance shiri ne mai kayatarwa, amma za mu ga basirar da Mata 100 da su zo da ita a wannan watan."

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Muna da wadansu labarai na karfafa gwiwa, inda za mu dubi wadansu abubuwa tara da ba kowa ba ne ya san cewa mata ne suka kirkiro su.

Kuma za mu duba wadansu hanyoyin da mutane suka fito da su wajen magance matsaloli kiwon lafiya da kare mata daga matsaloli.

Za a iya tuntubar mu a shafukanmu na Facebook da Instagram da Twitter da kuma ta hanyar amfani da maudu'in #100Mata