Ban san abin da ke damun Buhari ba - Lai Mohammed

A cikin wannan shekarar sau uku Shugaba Buhari na zuwa Landan Hakkin mallakar hoto NIGERIAN GOVERNMENT
Image caption A cikin wannan shekarar sau uku Shugaba Buhari na zuwa Landan

Ministan yada labaran Najeriya Alhaji Lai Mohammed ya ce bai san takamaiman abin da ke damun Shugaba Muhammadu Buhari ba ta bangaren lafiyarsa, don haka ba zai iya yi wa 'yan kasar karin bayani ba.

Alhaji Lai Muhammed ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da sashen Turanci na BBC Newshour.

Ga dai yadda hirar ta kasance:

Tambaya:Ko zan iya tambayarka dangane da shugaban kasa da yanayin lafiyarsa, inda ya zo nan London a makon da ya gabata, kuma ziyararsa ta uku kenan cikin shekara, inda a wancan karon ya shafe wata uku ana duba shi. To yaya lafiyarsa take?

Lai Mohammed: Ya samu sauki sosai, ya murmure.

Tambaya:To ko wacce irin cuta ce shugaban yayi fama da ita?

Lai Mohammed: Ina ganin cewa, shugaban ne kawai yake da ikon bayyaana ciwon da yayi fama da shi.

Tambaya:To ko kai kasan cutar da yayi fama da ita?

Lai Mohammed: Ban sani ba, kuma bana son na sani.

Da gaske, a matsayinka ministan watsa labarai?

Tambaya:Eh.

Tambaya:To menene yasa haka?

Lai Mohammed:Wannan wani abu ne da ya shafi shugaban kawai.

Tambaya:Amma wannan abu ne da yake da matukar muhimmanci da 'yan Najeriya zasu so su sani?

Lai Mohammed: Ina ganin koda a matsayinka na shugaban kasa, kana da ikon kare sirrinka, a wasu lokuta, kuma ina ganin babu wani abin sirri kamar yanayin lafiyar mutum.

Tambaya:Na fahimci wannan ikon, amma kuma akwai alhakin sanin wanda ke rike da ragama, wa yake tafiyar da abubuwa, ko zai iya rike shugabanci saboda rashin lafiya,inda ya shafe watanni uku anan London don neman sauki?

Lai Mohammed: Mr Frank, baa taba samun gibi na shugabanci a wannan gwamnatin ba, ba a taba samu ba, idan da an samu wani gibi, tattalin arzikin bazai taba farfadowa ba.

Da akwai gibin shugabanci lokacin da shugaban yake Birtaniya, da ba zamu samu nasarar da muka samu a bangaren yaki da rashawa da dawo da zaman lafiya a yankin Niger Delta ba, don haka babu wani gibi, lallai da mun ace yana nan, mun yi kewarsa, amma fa babu wani gibi da aka samu.

Tambaya:Da alama babban lamari ne, idan har shugaban bazai iya samun cikakkiyar kulawar lafiyarsa a kasarsa ba?

Lai Mohammed: Ba wani sabon abune ba, mutum ya yi ciwo na wata uku, sannan ya samu cikakkiyar lafiya.

Tambaya:Eh amma ba kamar shugaban babbar kasa kamar Najeriya ba?

Lai Mohammed: Gaskiyar lamarin shi ne, akwai shugabannin kasashe da yawa, da da wuya ake ganin su.

Tambaya:Misali kana nufin kamar su Zimbabwe?

Lai Mohammed: A'a, a'a bazan kira sunan kowacce kasa ba, abinda nake nufi shine babu wani laifi a rashin lafiya, da kuma samun sauki, tare da dawowa kan aiki.

Tambaya:Kana nufin ya samu sauki, ya murmure kenan.

Lai Mohammed: Eh tabbas shugaban kasa ya mumure sosai ma kuwa.