Las Vegas: An kashe mutum 59 a wani gidan rawa

Wadansu mutane lokacin da suke guduwa daga wurin Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wadansu mutane lokacin da suke guduwa daga wurin

Kusan mutum 60 ne suka rasa rayukansu yayin da wadansu kimanin 527 suka jikkata bayan wani hari da aka kai a wani gidan rawa a birnin Las Vegas na jihar Nevada da ke kasar Amurka.

Shugaba Trump ya bukaci Amurkawa su hada kai kuma su zauna lafiya, bayan aukuwar abin da ya kira harbe-harben tsagwaron k'eta.

Ya yi wannan kira ne daidai lokacin da 'yan sanda suka ce sun gano bindigogi guda 18 da nakiyoyi da dubban albarusai a gidan Stephen Paddock da suka ce shi ne ya kai harin da ya yi sanadin mutuwar mutum 59 a Las Vegas.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Yadda tashin hankalin ya kasance - cikin minti biyu

Dan bindigan, Stephen Paddock mai shekara 64 ya bude wuta daga hawa na 32 na otel din Mandalay Bay dake birnin Las Vegas ranar Lahadi a kusa da wani bikin wake-wake.

Masu bincike sun gano bindigogi 23 a dakin otel din da ya kama, kuma an sami wasu bindigogi da suka zarce guda 19 a gidansa dake jihar Nevada.

Kawo yanzu, babu wani dalili da ya bayyana na wannan aika-aikar ta Mista Paddock.

Maharin ya fara bude wuta ne daga hawa na 32 na benen wani otel mai suna, Mandalay Bay Hotel, inda ya hari wani wuri da ake wasan raye-raye.

'Yan sanda sun ce an harbe maharin wanda dan unguwar ne, kamar yadda suka ce.

Sai dai sun ce suna ci gaba da farautar wani wanda suke zargin yana aiki tare da maharin.

Daruruwan mutane sun tsere daga wurin kuma an rika jin karar harbe-harbe a wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta.

Hakazalika an samu rahotannin faruwar wadansu hare-hare a wasu bangare na birnin, sai dai 'yan sanda sun ce sun yi amannar cewa maharin shi kadai ne.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Wadansu mahalarta taron yayin da suke kokarin buya

Karanta karin wasu labaran

Wadansu jirage sun fasa sauka a birnin bayan samun labarin harin.

Tun ranar Juma'a ake ta shagulgulan raye-raye a otel-otel da ke birnin.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wadansu ma'aurata yayin da suke kokarin buya bayan fara harbe-harben
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wadansu 'yan sanda dauke da makamai a wajen otel din da aka kai harin
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Daruruwan mutane sun tarwatse yayin da aka fara harbin

Labarai masu alaka