Nwodo on IPOB
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Sauya fasali ya fi dacewa ba raba Nigeria ba – Ohaneze

Jama'a dadama a Najeriya na kiraye-kirayen sake fasalta kasar, ciki har da mutanen kudu maso gabashin kasar wadanda suke ganin sake fasalta kasar ne zai magance dumbin matsalolin da ake fama da su.

Wannan batun ne ma ya kai ga majalisar wakilan Najeriya ta kafa wani kwamiti domin duba batun.

Cif John Nwodo shi ne shugaban kungiyar. Ya ziyarci ofishinmu na Landon a kwanakin baya, ya kuma tattauna da Editan Sashin Hausa na BBC, Jimeh Saleh a kan abin da ya sa suke goyon bayan sake fasalin mulki a Najeriya, da kuma adawar da suke yi da ballewar yankin Biafra daga kasar.

Ya bayyana cewar sauya fasalin Najeriya shi ya fi dacewa da muradun 'yan kabilar Igbo na nan gaba maimakon fafatukar kafa kasar Biafra.

Za ku iya sauraron cikakkiyar hirar da Editan BBC Hausa Jimeh Saleh ya yi da John Nwodo, idan ku ka latsa alamar lasifika da ke sama.

Labarai masu alaka