Hotunan abin da ya faru a Afirka a makon jiya

Wasu daga cikin kyawawan hotuna daganahiyar Afirka da kuma na 'yan Afirka dake zaune a wasu sassan duniya a makon da ya gabata.

Wadansu Kiristoci yayin wani bikin Meskel na addinin Kirista a babban birnin kasar Habasha, Addis Ababa Hakkin mallakar hoto Reuters

Wadansu Kiristoci yayin wani bikin Meskel na addinin Kirista a babban birnin kasar Habasha, Addis Ababa.

A choir member blows a traditional trumpet during the Meskel Festival Hakkin mallakar hoto Reuters

Wani yaro yayin da ke busa wani kahon karfe lokacin bikin addinin ranar Talata.

An Ethiopian Orthodox deacon carries a cross during the Meskel Festival to commemorate the discovery of the true cross on which Jesus Christ was crucified on at the Meskel Square in Addis Ababa, Ethiopia Hakkin mallakar hoto Reuters

Wadansu matasa da suka halarci bikin.

Wata mata 'yar kasar Senegal tsugune a gaban wani kabari ranar Talata yayin cika shekara 15 da nutsewar wani jirgin ruwa mai suna Joola. Hakkin mallakar hoto AFP/Getty Images

Wata mata 'yar kasar Senegal tsugune a gaban wani kabari ranar Talata yayin cika shekara 15 da nutsewar wani jirgin ruwa mai suna Joola.

Akalla mutum 1,800 suka mutu lokacin da jirgin ruwan ya nutse a shekarar 2002, adadin ya zarta na wadanda suka mutu lokacin da jirgin ruwan Titanic ya yi hadari a shekarar 1912. Hakkin mallakar hoto AFP/Getty Images

Akalla mutum 1,800 suka mutu lokacin da jirgin ruwan ya nutse a shekarar 2002, adadin ya zarta na wadanda suka mutu lokacin da jirgin ruwan Titanic ya yi hadari a shekarar 1912.

A woman looks at an exhibit in the main hall of the Zeitz Museum of Contemporary African Art in Cape Town on September 22, 2017. Hakkin mallakar hoto AFP

Wata mata tana kallon wadansu kayayyaki da aka baje kolinsu a wani bikin baje koli mafi girma na zamani a birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu.

Wadansu mutane da suka halarci bikin baje kolin. Hakkin mallakar hoto AFP

Wadansu mutane da suka halarci bikin baje kolin.

Pastor Evan Mawarire holds a Zimbabwean flag as he is escorted to the police cells, in Harare, Zimbabwe, September 26, 2017 Hakkin mallakar hoto Reuters

Wani limanin Kirista Evan Mawarire rike da tutar kasar Zimbawea lokacin da 'yan sanda suka tasa keyarsa zuwa caji ofis ranar Talata. Ana tuhumar Fasto Mawarire da laifin sukar gwmanati Shugaba Robert Mugabe kan hanyoyin da take bi wajen shawo kan matsalar tattalin arzikin kasar.

Wani mutum lokacin da yake wanke goro a birnin Anyama na kasar Kwaddibuwa ranar Litinin. Kwaddibuwa ita ce kasa ta biyu da take kan gaba wajen samar da goro Hakkin mallakar hoto AFP

Wani mutum lokacin da yake wanke goro a birnin Anyama na kasar Kwaddibuwa ranar Litinin. Kwaddibuwa ita ce kasa ta biyu da take kan gaba wajen samar da goro.

Wadansu mata suna jan akalar rakuma lokacin da Shugaba Omar al-Bashir na Sudan ya kai ziyara garin Umm al-Qura na yankin Darfur a makon jiya. Hakkin mallakar hoto AFP/Getty Images

Wadansu mata suna jan akalar rakuma lokacin da Shugaba Omar al-Bashir na Sudan ya kai ziyara garin Umm al-Qura na yankin Darfur a makon jiya.

Sudanese President Omar al-Bashir delivers a speech during a visit to the village of Shattaya in South Darfur Hakkin mallakar hoto AFP/Getty Images

Shugaba al-Bashir lokacin da yake jawabi a kauyen Shattaya na yankin Darfur

Hotuna daga AFP da EPA da PA da kuma Reuters

Labarai masu alaka