An fara gwajin sabuwar riga-kafin mura

flu vaccine Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Riga-kafin daban ce da wadd ake da ita yanzu, inda tsohuwar ake sabunta ta duk shekara

Masu bincike a Burtaniya na guanar da abin da suka kira wani hamshakin gwaji na wata sabuwar allurar riga-kafin cutar mura.

Masu sa-kai kimanin 500, kama daga 'yan shekara 65 zuwa sama ne za a yi wa allurar ta gwaji.

An hada wannan allurar riga-kafi ce ta yadda za ta iya aiki don kashe nau'o'in cutar mura da dama.

Sabuwar allurar na karfafa garkuwar jikin dan'adam ta yadda za ta iya kai farmaki ga sinadaran ginan jiki da ke can cikin kwayoyin cutar virus na mura.

Riga-kafin kuma za ta ba wa jiki kariya tsawon shekaru.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sabuwar riga-kafin na amfani da wata hanya mai ban mamaki don raba jiki da mura.

Allurar riga-kafin da ake da ita yanzu tana tunkarar sinadaran gina jiki na proteins a saman fatar kwayoyin cuta ne.

Kuma masu bincike sun yi hasashen sake yunkurowar murar da za ta shiga cikin jama'a don haka suka ga bukatar sake fasalin riga-kafinta kowacce shekara.

Ana fatan cewa sabuwar allurar riga-kafin za ta kashe zafin cutar a tsakanin mutanen da aka yi wa riga-kafi amma mura ta ci gaba da addabarsu.

Labarai masu alaka