Nigeria: Alkali ya janye daga shari'ar 'yan Boko Haram

Boko Haram Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu ta da kayar bayan Boko Haram sun raba miliyoyin mutane daga muhallinsu

Wani alkalin kotun tarayya a Najeriya ya janye daga shari'ar wasu da ake zargin 'ya'yan kungiyar Boko Haram ne.

Wasu daga cikin mutanen, wadanda ake tsare da su a hannun jami'an tsaro na farin kaya (DSS) ne suka bayyana rashin amincewa da Mai Shari'a John Tsoho na kotun tarayya ta Abuja.

Sun kuma koka kan yadda aka ki ajiye su a gidan jari kamar takwarorinsu da ake zargi.

A zaman kotun na ranar Talata, Mai Shari'a Tsoho ya mika shari'ar mutum takwas, da ake zargi da aikata da aikata laifukan ta'addanci, ga babban jojin kasar.

Mutanen sun kara da cewa yanayin zaman gidan yarin ya fi na ofishin jami'an DSS dadin sha'ani don sun kamu da rashin lafiya sakamakon kasancewarsu a hannun jami'an na DSS.

Amman wadanda suke gidan yari cikin mutanen sun shaida wa alkalin cewar su sun amince da alkalancinsa.

Sai dai duk da haka, mai shari'a John Tsoho ya ce ba zai dace shi ya cigaba da alkalancin shari'arsu ba tun da wasunsu ba su amince da alkalancinshi ba.

A ranar 14 ga watan Maris ne kotun ta ba da umarnin a ajiye mutanen da ake zargi da aikata laifukan ta'addancin a gidan yari.

Amman gwamnati ta nemi a ajiye wasu daga cikinsu cikin a hannun jami'an DSS domin gwamnatin na ganin cewa kasancewarsu a gidan yari ka iya haifar da barazanar tsaro.

Daga baya sai aka mayar da wassu daga cikinsu hannun jami'an tsaro na farin kaya, lamarin da ya sa wadanda ake zargin suka ce ba su amince da alkalancin mai shari'an ba.

Labarai masu alaka