Mancherster United 'za ta nemi Mesut Ozil'

Mesut Ozil Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mesut Ozil ya koma Arsenal ne a shekarar 2013

Rahotanni a Ingila na cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za ta nemi dan wasan Jamus Mesut Ozil a watan Janairu.

Labarin da jaridar the Independent ta wallafa yana zuwa ne a daidai lokacin da ake kwan-gaba-kwan-baya kan sabuwar yarjejeniya tsakanin dan wasan da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal.

Mesut Ozil ya koma Arsenal ne daga Real Madrid kan kudi fam miliyan 42.4 a shekarar 2013.

Yana daga cikin manyan 'yan wasan kungiyar da sukan sha suka a duk lokacin da ba ta yi katabus ba.

Sai dai ya sha nanata irin rawa da kuma kokarin da shi da sauran 'yan wasan kulob ke takawa a duk lokaicn da aka bujuro da irin wannan zargi.

Labarai masu alaka