Amurka ta hana bayar da magungunan hana daukar ciki

Kungiyoyin mata a Amurka na adawa da matakin hana bayar da magungunan hana daukar cikin a kasar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kungiyoyin mata a Amurka na adawa da matakin hana bayar da magungunan hana daukar cikin a kasar

Gwamnatin Shugaba Trump na Amurka ta sanar da wasu sabbin dokoki da za su hana wa matan kasar kusan miliyan 60 samun magungunan hana daukar ciki.

Ma'aikatar lafiya ta Amurka ta ce, yanzu ma'aikatu da kamfanonin inshora za su iya tsame kansu daga samar da magungunan hana daukar cikin da ma wasu hanyoyin takaita haihuwa.

A da ana bayar da irin wadannan magungunan a karkashin tsarin kula da lafiya na gwamnatin Shugaba Obama.

Wannan sanarwa dai ta samu karbuwa daga wasu masu tsattsauran ra'ayin addini, amma kuma wasu kungiyoyin mata sun soki matakin Shugaba Trump din na hana bayar da magungunan hana daukar cikin.

Tuni da ma dai kungiyoyin kare hakkin dan adam na Amurka suka shigar da kara kotu inda suke kalubalantar wannan mataki.

Labarai masu alaka