Tankokin mai sun kama da wuta a Tafa kusa da Abuja

Lorry tanker fire Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An sha samun gabora irin wannan a Nigeria

Wata mummunar gobarar ta katse zirga-zirga a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a garin Tafa inda manyan motoci ke yada zango, a jihar ta Kaduna, dake arewa maso yammacin Najeriya.

Ganau sun shaida wa BBC cewar akalla tankokin mai uku ne suka kone a gobarar, lamarin da ya sa matafiya akan hanyar suka ringa sauya akala zuwa hanyar Jere.

A halin yanzu dai 'yan kwana-kwana sun kashe wutar, kuma motoci sun fara wucewa.

Har yanzu dai ba a tabbatar da adadin asarar rayukan da aka yi ba a gobarar, amman wasu rahotanni sun ce gobarar ta haddasa asarar rayuka ta kuma kona wasu gidaje.

Garin na Tafa ya zama wajen yada zango na manyan motocin dake jigilar mai da tsakanin kudanci da arewacin kasar, inda dirobobi kan ajiye motocinsu a gefen hanya.

Yawan ajiye manyan motocin a garin yakan haddasa cinkoso a kan hanyar, lamarin da yake sa matafiya suke bata lokaci a wajen.

Labarai masu alaka