Nigeria: 'Yan sanda na tuhumar Davido kan mutuwar abokinsa

Davido Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Davido ya bayyana alhininsa a shafin Istagram kan mutuwar Tagbo Umeike

'Yan sanda a Najeriya sun ce suna binciken fitaccen mawakin zamanin nan David Adedeji Adeleke (Davido) domin neman bayanai kan mutuwar abokinsa.

Tagbo Umeike ya mutu ne ranar 3 ga watan Oktoba, kuma ba a gane musabbabin mutuwarsa ba duk da cewar bincike ya nuna cewa ya mutu ne sakamakon shake shi da aka yi.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Legas, Olarinde Famous-Cole, ya ce rundunar 'yan sandan ta yi kira ga Davido da 'yan uwansa da kuma abokan Tagbo Umeike su bayyana a gaban ofishin 'yan sandan.

Famous-Cole ya shaida wa BBC cewa: ''Abin da muke yi yanzu shi ne muna son mu san tare da waye Tagbo yake kuma ina ya je ranar da ya mutu?''

''Wani hoton bidiyo da wasu bayanai sun fito kuma a yanzu muna kiran sauran mutane ciki har da Mista Adeleke domin tambayoyi saboda mu gane hakikanin abun da ya faru.''

'Yan sanda sun ce wannan wani bincike ne da ake ci gaba da yi, kuma ba za su iya kara bayani game da ko Davido na da hannu a ciki ko babu ba, har sai an samu kwararan hujjoji game da abin da ya kashe Mista Tagbo.

Wakilin BBC a Legas ya ce tuni Davido ya bayyana a ofishin 'yan sanda domin amsa tambayoyi, kuma bayanai sun nuna cewa an sake gayyatarsa.

Har wa yau wani abokin Davido, Olugbemiga Abiodun, wato DJ Olu, ya mutu kwanaki bayan mutuwar Tagbo.

'Yan sanda sun ce da 'walakin goro a miya' dangane da mutuwarsa ba.

Sun samu gawar DJ Olu da Chime Amechina a cikin mota a wani garejin karkashin kasa a unguwar Ikoyi.

Davido ya wallafa sakonnin juyayin rasuwar abokanan nasa a shafin Instagram.

'Yan sanda sun ce in suka kammala bincike, za su sanar da mutane hakikanin abin da ya faru.

Mutuwar ta Umeike ta haifar da rudani a Legas, inda jama'a musamman magoya bayan mawakin ke bayyana ra'ayoyi daban daban.