Karnukan Amurka 'sun fi mutanen Nigeria' gata a asibitoci

A patient lies on their back in a radiotherapy machine in Khartoum. Hakkin mallakar hoto AFP

Ikirarin: Kare a Amurka ya fi samun damar a yi masa gashin cutar sankara fiye da mutum a Najeriya.

Gaskiyar lamarin: Na'u'rorin kashe kwayoyin cutar sankara da ake da su domin mutane a Najeriya ba su kai wadanda aka tanada domin karnuka a Amurka ba.

Amman sai dai dabbobi 'yan lele masu dauke da cutar sankara a Amurka sun fi mutane masu cutar samun gata a Najeriya - kuma na'u'rorin kona cutar sankara da ake da su na dabbobi kawai sun fi na wadanda ake amfani da su gutanen Najeriya.

A watan da ya gabata ne, Sean Murphy ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sa da zumunta.

Dan kasuwar ya wallafa wani hoton kare da yake amfani da wata irin na'u'rar konaa cutar sankara, kuma ya ce irin wadannan na'u'rorin da ke yi wa karnukan Amurka magani sun fi wadanda suke yi wa 'yan Najeriya magani.

Ya ce wannan na nufin kare a Miami ya fi wata mata a Legas damar samun maganin sankara. Maganar tasa ba ta zo wa mutane da dama da mamaki ba, amman duk da haka ta fusata su.

Amman da alamar gaskiya a ikirarin nasa? Shin karnukan Amurka sun fi 'yan Najeriya damar samun na'u'rar kona sankara?

Kayan aiki

Ba ko wanne mai cutar sankara ke bukatar gasa sankara ba - akwai wasu nau'o'i na magani, irin su hanyar shan magani domin dakile cutar sankara.

Amman ikirarin Mista Murphy ya yi ne kan damar samun na'u'rar kona sankara, saboda haka bari mu tsaya a kan wannan na'urar kawai.

Hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya tana da jerin sunayen wuraren da ke da na'u'rorin gasa sankara a fadin duniya.

Matattarar bayanan cibiyoyin na'urorin gasa sankara ta hukumar (Dirac) tana samun bayanai ne daga kasashe daban-daban. Amman a makon da ya gabata ne kawai aka tattara bayanai na baya-bayan nan.

Matattarar ta ce abun ya fi yadda Mista Murphy ya bayyana shi muni.

Nau'rorin gashi uku ne ke aiki a Najeriya a halin yanzu, kuma babu na zamani irin wanda Mista Murphy ya ambato a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Dirac ta ce a kan hada na'ura ta hudu a Abuja, kuma wannan din ma ba za ta kasance irin ta zamani da Murphy ya ambata ba.

Akwai karin na'u'rori da ake amfani da su wajen shirya ba da magani irin su na'u'rorin daukar hoton kashi.

Kuma Dirac ta ce babu wata cibiyar ba da magani da ta sani da take bai wa mara lafiya gashi kan dashe, wadda ita ce hanyar ba da maganin cuta irin sankarar mahaifa.

Babu tabbacin karin na'u'rorin nawa ne za a iya samu a asibitoci masu zaman kansu - amman jaridar The Nation ta ce wadannan sun fi karfin mara sa galihu.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yawan na'u'ro'rin ga mutane ya fi na Najeriya yawa sau tara a Kenya

Bayanai daga bankin duniya sun nuna cewar yawan mutane a Najeriya ya kai miliyan 186. Da zarar an kammala hada na'u'rar ta hudu, za a samu na'urar gashi daya ga mutum miliyan 46.5 a Najeriya.

Idan ma na'urori takwas da Najeriya ta ke da ita a shekarar 2010 suna aiki har yanzu - adadin mutanen da za su dogara da na'u'rar gashi daya zai kai mutum miliyan 23.2 .

A Kenya, akwai na'urar gashi daya ga mutum miliyan 5.4 million.

A Indiya kuma mutum miliyan 2.2 suna da na'ura daya, ga mutum 188,000 suna da na'urara gashi daya a Birtaniya yayin da mutum 84,000 ke da na'urara gashi daya a Amurka.

Ta yaya lamarin yake idan aka kwatanta da karnukan Amurka?

Kona cutar sankara a jikin maguna da karnuka

Muna son dabbobin lelen Amurka suna da damar samun na'u'rorin gashi fiye da na'urorin da ake da su a Najeriya - a shekarar 2010, wani bincike da Margaret McEntee da John Farrelly suka gudanar ya kirga irin na'urar gashin da ke Najeriya, a kalla 76 suna yi wa dabbobi hidima a fadin Amurka.

A gaskiya, wata matattarar bayanai da kungiyar likitocin cutar sankarar ta nuna cewa mai yiwuwa ne adadin na'urorin ya fi na adadin da aka sani yanzu.

Cibiyar cutar sankara ta Amurka ta ce akwai karnuka 'yan lele miliyan 65 a Amurka.

Wannan na nufin cewa a kalla akwai na'ura daya ga maguna da karnuka miliyan 1.28 a Amurka.

Wa yake bukatar magani?

Amman kwatanta adadin na'urori da yawan mutane da dabbobi ka iya gaza taimakawa kan wannan batun.

Hakan ya faru ne saboda dabbobin lele sun fi mutane yiwuwar kamuwa da ciwon sankara.

Kimanin maguna da karnuka miliyan 12 suna kamuwa da cutar sankara a ko wacce shekara - wannan na nufin akwai na'urar gwaji ga karnuka da maguna 158,000 masu cutar sankara.

Alkaluma na baya-bayan nan daga Hukumar Lafiya ta Duniya sun ce an gane cewa mutum 102,100 sun kamu da cutar sankara a Najeriya cikin shekarar 2012.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dirac ta ce ana hada wata na'urara gashi a asibitin taryyar Najeriya ta Abuja - amman rashin na'ura ba sh8i kadai ne yake hana 'yan Najeriya samun gashi na sankara a kasar.

Ga dabbobin lelen Amurka da mutanen Najeriya tsadar rayuwa wani abu ne da ke hana samun magani ko na'urorin na aiki.

Gashi ga dabbar lele ka iya kai kudi $10,000 - abun da kila ya sa binciken John Farrelly ya nuna cewa karnuka 1,376 dogs da maguna 352 aka yi wa gashi a Amurka a shekarar 2010.

Kazalika, wani bincike da aka gudanar a asibitin koyarwa na jami'ar Ibadan ya nuna cewa takwas daga cikin masu cutar sankara goma a Najeriya ba za su iya biyan kudin gashi ba ba tare da taimako ba, inshorar gwamanti ba ta daukar nauyinsa.

Mun tambayi gwamnatin Najeriya ta yi tsokaci kan karancin na'urorin gashi masu aiki, amman har yanzu ba ta ce ko uffan ba.

A wani taro a Abuja da aka yi da farkon watannan, ministan lafiyar Najeriya, Isaac Adewole ya ce gwamantin kasar ta tsaya tsayin daka domin ganin ta dakile cutar sankara a Najeriya. Ya yi alkawarin cewa za a kara na'urori takwas zuwa sha biyu, amman ba bu tabbacin nawa ne daga cikinsu za su kasance na gashin sankara.

Samun na'urar kona cutar sankara mai aiki babbar matsala ce a fadin Afirka.

Matsalar Najeriya gagaruma ce domin a yanzu haka na'urorin kona cutar sankara uku kadai take da su da ke aiki a halin yanzu.Labarai masu alaka