Shugaban kamfanin Samsung ya yi murabus

Ana dai zargin shugaban Samsung din da aikata cin hanci Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana dai zargin shugaban Samsung din da aikata cin hanci

Shugaban kamfanin kere-keren kayan lantarki na Koriya ta Kudu, Samsung, ya sauka daga mukaminsa.

Kwon Oh-Hyun, ya ce lokaci ya yi da kamfanin zai bude sabon shafi tare da matashin shugaba.

Hakan ya biyo bayan hukuncin daurin shekaru biyar a kurkuku da aka yi wa tsohon shugaban kamfanin, Jay Lee, a watan Agusta bisa laifin cin hanci da rashawa.

An dai sa ran Mr Kwon zai ci gaba da taka muhimmiyar rawa a kamfanin.