'Dalibi ya kashe 'yan uwansa dalibai biyar a Kenya'

A map of Kenya

Akalla dalibai biyar da wani mai gadi sun mutu sakamakon wani hari da aka kai wata makarantar kwana a arewacin kasar Kenya.

Shugaban makarantar AIC Lokichogio Secondary School ya ce suna zargin wani dalibi wanda aka dakatar daga makarantar da jagorantar harin.

Ana zargin cewa dalibin tare da wadansu mutane biyu ne suka kai harin a ranar Asabar.

Wani ganau ya ce bayan kashe mutum shida, sun yi wa wadansu 'yan mata biyu fyade da kuma jikkata wasu dalibai 18.

Kamar yadda shugaban makarantar ya ce yaron ya fito ne daga kasar Sudan ta Kudu kuma an dakatar da shi ne saboda ya yi fada da wani dalibi.

Sai dai yayin harin abokin fadan na shi ba ya makaranta a lokacin.

Jaridar Daily Nation ta ruwaito cewa dalibin da ake zargin ya taba shaida wa "takwarorinsa dalibai cewa zai kona makarantar ko kuma zai dawo ya dauki fansar dakatar da shi da aka yi".

Karanta wadansu karin labarai

Labarai masu alaka

Karin bayani