George Weah ya kai zagaye na biyu a zaben Liberia

george Weah Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption George Weah ya samu kashi 39 cikin 100 na kuri'un da aka kada

Tsohon shahararren dan wasan kwallon kafar Laberiya, George Weah, zai fafata da mataimakin shugaban kasar, Joseph Boakai, a zageye na biyu na zaben shugaban kasar.

Hukumar zaben kasar ta ce ta kammala kidayan kusan dukkannin kuri'un da aka kada a zaben da aka gudanar a ranar Talatar da ta wuce.

Mista Weah, wanda shi ne dan wasan kwallon kafar Afirka da ya taba lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya, ya samu kashi 39 cikin 100 na kuri'un da aka kada.

Shi kuma Mista Boakai ya samu kaso 29 cikin 100.

Ana sa ran a watan gobe ne za a gudanar da zagaye na biyu na zaben.

'Yan takara 20 ne suka fafata a zagayen farko na zaben domin maye gurbin Shugaba Ellen Johnson Sirleaf, wadda ita ce shugabar kasa mace ta farko a nahiyar Afirka.

Sai dai har yanzu akwai wuraren da ba a kammala kidaya kuri'unsu ba.

Duka 'yan takarar biyu da suke kan gaba sun yi tsammanin lashe zaben a zagayen farko.

Abin da ya sa har tsohon kocin Mista Weah wato Arsene Wenger, ya yi hanzarin taya shi murnar lashe zaben bayan samun wadansu rahotannin bogi wadanda suka ce dan wasan ne ya lashe zaben.