Yadda girgizar kasa ta shafe kauyuka daga doron kasa a Iran

Building damaged by earthquake in Iran Hakkin mallakar hoto Khosrow
Image caption Girgizar kasar ta lalata gine-gine da dama, inda daruruwan mutane suka mutu, da dama kuma suka jikkata

Hotunan yadda bala'in ya faru sun fara bayyana a yankin da ke kan iyakar kasar Iran da Iraki, bayan faruwar girgizar kasar mai karfin maki 7.3 a ranar Lahadi da yamma.

Ganau da suka yi magana da BBC sun yi ta bayyana yanayin da suka samu kansu a ciki sakamakon motsin kasar.

Khosrow: 'Kanwar mahaifiyata da 'yarta da jikokinta sun mutu'

Hakkin mallakar hoto Khosrow
Image caption Dangin Khosrow da dama sun mutu sakamakon girgizar kasar

Khosrow na zaune ne a wani kauye kusa da Sarpol-e Zahab, daya daga cikin wuraren da abin ya fi yin ta'adi, dab da kan iyakar Iraki.

Ya ce duk danginsa sun mutu kuma kauyen ya lalace.

"Gini ya yi ta ruftowa kan mahaifina da kannena mata. Haka na yi ta janye su daga gidan.

Ya ce: "Mahaifiyata ta ji rauni. Kanwar mahaifiyata da 'yarta da jikokinta duk sun mutu."

"Illahirin kauyen ya ruguje.

"Kaburbura sun yi ta budewa har wasu gawarwaki suka dinga fitowa daga ciki.

"Ba ruwa. Mutane na amfani da ruwan kogi. Ba mu da abinci. Ba mu da ruwan sha da kayan sanyi."


Amir: 'Ina zaton yawan wadanda suka mutu zai karu'

Hakkin mallakar hoto Alireza
Image caption Asarar da girgizar kasar ta jawo na da yawa

Amir na zaune ne a garin Sarpol-e Zahab. Ya ce kashi 30 cikin 100 na garin ya lalace.

"Kashi 30% na gine-ginen da ke garin sun rushe.

"Mutane na bukatar abinci da ruwa. Masu ceto sun zo garin amma dai ina zaton yawan wadanda suka mutu zai karu."


Mehrdad: 'Kauyuka sun shafe daga doron kasa'

Hakkin mallakar hoto UGC
Image caption Girgizar kasar ta shafe dumbin gidaje daga doron kasa

'Yan uwan Mehrdad na samun mafaka ne a yankin Kermanshah cikin sansanoni bayan da gidajensu suka lalace.

Ya ce: "Na ziyarci kauyuka a kusa da tsakiyar inda girgizar kasar ta afku a Kermanshah, don na kai wa 'yan uwana abinci da tanti."

"Duk kauyukan sun shafe kamar ba a yi su ba.

"Mutane ba su da isasshen abinci da ruwa da sauran kayan bukatu."


Salah: 'Mutane na zaune a filin Allah'

Hakkin mallakar hoto Salah
Image caption Mutane na zaune a cikin tantuna a Kermanshah, amma dai suna cikin tsananin bukatar abubuwan amfani na yau da kullum

Salah na zaune ne a Salas-e Babajani, da ke gundumar Kermanshah.

Ya ce: "Muna kusa da tsakiyar inda al'amarin ya faru.

"Mutane na zaune ne a filin Allah.

"Babu isassun tantuna da za su fake, kuma kashi 50 zuwa 80 cikin 100 na gidajen garin sun rushe.

"Babu abinci kuma babu magani."

Labarai masu alaka

Karin bayani