Fasto ya sa mabiyansa cin kyankyaso a Afirka Ta Kudu

End Times Minsitries Hakkin mallakar hoto End Times Minsitries
Image caption A shekarar 2015 ne wannan fasto ya umarci mutane su ci maciji da beraye da kuma gashi

Wani fasto a Afirka Ta Kudu Penuel Mnguni, ya sa wasu mabiyansa biyu 'yan uwan juna sun ci kyankyasai.

Faston, wanda aka fi sani da 'Fasto Mai Maciji," ya yi ikirarin cewa idan suka ci to ba wai kyankyaso suka ci ba, ji za su yi kamar sun ci cukwi da kayan kamshi.

Wannan al'amari dai ya faru ne watanni biyar bayan da Mista Mnguni ya halarci cocin wani shahararren fasto a Najeriya TB Joshua, inda a can din ya yi ikirarin cewa, "bai wa mutane naman maciji su ci ba shi da halacci a addinin kirista.

Hakkin mallakar hoto TB Joshua Twitter
Image caption Sakon da TB Joshua ya wallafa a shafinsa na Twitter

Fasto Joshuwa ya wallafa sako a shafinsa na Twitter cewa: "Fasto mai maciji daga Afirka Ta Kudu ya yi ikirarin cewa bai wa mutane naman maciji su ci ba shi da tushe a littafin injila. Mene ne ra'ayinku kan hakan?"

Cocin Mista Mnguni ya wallafa wani sako a shafin Facebook kan batun cin kyankyason a farkon watan nan, inda sakon ya ce faston ne ya kira kyankyasai sai kuwa suka bayyana a cocin."

Sakon ya ce: "Daga nan sai ya kira mabiyansa don su matso su ci .... Sai wasu 'yan uwan juna biyu suka dauka suka ci, a yayin da suke ci ne sai wani abu ya bai wa daya daga cikin su, Mista Charles mamaki, inda ya ji dandanon kyankyason ya yi kama da na cukwi.

"Shi kuwa Mista Eric sai ya ji dandanon kamar na kayan kanshi da ake girki da su," a cewar sakon.

Hakkin mallakar hoto End Times Dicsiples Ministries

Sakon ya kara cewa: "Fasto ya ce cin kyankyason nan da suka yi zai kara musu kaifin sani kuma za su sauya su fi yadda suke a da."

Wani sako da cocin ya sake wallafa kuma ya ce, faston ya yi addu'a kan wata fulawa mai guba, sai wani mabiyinsa ya ci, ya kuma ji dadinta ta yadda har sai da ya roki a bar shi ya cinye fulawar baki dayanta.

Sakon ya ce: "Ubangiji ya yarjewa fasto kan duk abun da ya nema.

A shekarar 2015 ne wannan fasto ya fara jawo ce-ce-ku-ce a Afirka Ta Kudu bayan da ya umarci mutane su ci naman maciji da beraye da kuma gashi.

A watan Yulin 2015 din ne kuma aka janye wata kara da Hukumar da ke kare hakkin dabbobi ta shigar kan Fasto Mnguni, saboda rashin hujjoji.

Hakkin mallakar hoto End Times Dicsiples Ministries