Da ma Atiku bakunta ya je jam'iyyar APC — PDP

Jam'iyyar PDP a Najeriya, ta ce Atiku Abubakar, gida ya dawo da ma bakunta yaje
Image caption Jam'iyyar PDP a Najeriya ta ce Atiku Abubakar gida ya dawo da ma bakunta ya je yi APC

Babbar am'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar gida ya dawo, da ma bakunta ya je yi a jam'iyyar APC.

Jam'iyyar PDP dai ta yi wannan magana ce sakamakon sauya sheka da Atiku Abubakar ya yi daga APC zuwa tsohuwar jam'iyyarsa ta PDP a makon da ya gabata.

Barista Abdullahi Jalo, wanda shi ne mai ba wa shugaban jam'iyyar na riko Ahmed Makarfi, shawara kan harkokin watsa labarai na Hausa, ya shaida wa BBC cewa, dama bakunta Atiku Abubakar din ya je jam'iyyar APC mai mulki, 'amma yanzu da ya ke lokaci ya yi ai ya dawo gida.'

Dangane da rade-radin da ake yi cewa tsohon mataimakin shugaban Najeriyar ya koma jam'iyyar PDP ne don ya nemi takarar shugabancin kasar, Barista Jalo ya ce: "Mutane na fadar hakan ne ba tare da la'akari da abin da kundin tsarin mulkin jam'iyyarmu ya tanada ba, da kuma matsayin da ake ciki a yanzu."

Don haka ya ce, ya kamata mutane su daina riga malam shiga masallaci a kan abin da ba su da tabbas, 'kuma shi Atiku Abubakar din ya fadi cewa zai tsaya takara ne?' In ji Barista Jalo.

Alhaji Atiku Abubakar, ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki ne tun a watan jiya inda ya ce jam'iyyar "ta kasa cika alkawuran da ta yi wa al'ummar kasar musamman matasa."

Don haka ya koma jam'iyyar PDP ne kuma saboda matsalolin da suka sa ya fice daga ita a shekarar 2014, an warware su yanzu.

Labarai masu alaka