Garabasa ga mai son aiki da BBC Hausa

Wannan damar za ta sa mai rabo ya zama daya daga cikin ma'aikatan Sashen BBC Africa
Image caption Wannan damar za ta sa mai rabo ya zama daya daga cikin ma'aikatan Sashen BBC a Africa

BBC ta fitar da wata sabuwar dama ga masu sha'awar aiki da sashenta na Hausa a Najeriya.

Damar ita ce ta aikin dan jarida mai daukar hoton bidiyo tare da sarrafawa domin wallafawa a shafukan intanet ko kuma domin watsa wa a talabijin.

Ana bukatar mai sha'awar wannan aikin ya iya bincike da tsarawa tare da kuma sarrafa ko hada labarai na bidiyo.

Duk wanda ya samu nasara, zai rinka yin aikin ne a katafaren sabon ofishin BBC da ke birnin Legas. Latsa nan domin neman aikin.

Bugu da kari ana son wanda zai yi wannan aikin ya iya kirkiro sabbin hanyoyin wallafa labarai kan shafukan sada zumunta da suka hada da Facebook da Twitter da Instagram da manhajojin aika sako da dai sauransu.

Har ila yau ana bukatar wanda zai yi wannan aikin ya iya bayar da gudummawa a zaman shirya yadda za a hada labarai na ko wacce rana.

Mai sha'awar aikin yana kuma bukatar iya sarrafa hotuna da taswira cikin gaggawa domin kara haske game da labarin da ke faruwa da kuma labarai masu sarkakiya.

Image caption Wannan damar dai za ta bai wa mai sa'a aiki da BBC a Legas

Kazalika ana son mai sha'awar aikin ya iya Hausa a rubuce da kuma a karance tare da iya amfani da manhajar Q-edit ko kuma Final Cut ProX ta sarrafa bidiyo.

Ana son kuma mai sha'awar aikin ya kware a aikin jarida tare da sanin wuraren da masu mu'amala da BBC Afrika suke ta bangaren siyasa da tarihi da al'ada da kuma yadda abubuwan da masu mu'amala da kafar ke so suke sauyawa.

Za a rufe wannan damar ne ranar Lahadi 10 ga watan Disambar 2017.

Labarai masu alaka