Trump ya mayar da Kudus a matsayin babban birnin Israila

Mr Trump ya bayyana matakin a matsayin wani abu da aka dade ba a yi ba Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mr Trump ya bayyana matakin a matsayin wani abu da aka dade ba a yi ba

Shugaban Amurka Donald Tump ya ce daga yanzu Amurka ta dauki birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar Isra'ila.

Da yake magana a fadar White House, Mr Trump ya bayyana matakin a matsayin wani abu da aka dade ba a yi ba a kokarin karfafa zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

Shugaban kasar ya ce Amurka za ta goyi bayan masalaha ta hanyar samar da kasashe biyu matukar Israila da Palasdinawa suka amince da shi.

Gabanin yanke shawarar, kakakin shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas ya yi gargadin cewa matakin yana da hadarin gaske ga yankin.

Tun da farko shugaba Trump ya kira wasu shugabannin kasashen Larabawa ta wayar tarho a ranar Talata, domin ya fada musu aniyarsa.

Ya kuma ce zai umarci ma'aikatar harkokin wajen kasar sa da ta fara kokarin mayar da ofishin jakadancin su zuwa birnin Kudus din daga Tel Aviv.

Sai dai Sarki Salman na Saudiyya ya fada masa cewa duk wani yunkuri irin wannan zai harzuka musulmi a kasashen duniya.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sarki Salman ya gargadi Trump kan kokarin harzuka musulmi a kasashen duniya.

Ita ma kungiyar Tarayyar Turai ta yi gargadi a kan duk wani mataki da ka iya kawo nakasu a kokarin da ake wajen ganin an cimma maslaha tsakanin Israila da Palasdinu.

Amma tun farko mai magana da yawun fadar White House Sarah Sanders, ta ce Shugaba Trump ya ce zai ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki kan lamarin idan ya dauki wannan mataki.

Isra'ila dai ta dauki birnin Kudus a matsayin babban birinin kasar, yayin da Falasdinu sun ayyana gabashin Kudus a matsayin wurin da zai kasance babban birninsu idan sun kafa tasu kasar.

Amincewar da Amurka ta yi wa Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila, ya sa ta kasance kasa ta farko da ta yi haka tun bayan kafuwar Israilar a shekarar 1948.

Labarai masu alaka