Asibiti ya biya dangin matar da ya ƙi kashewa diyya

Mrs Grant
Image caption An bar ta da ranta duk da ta ce ba ta son haka a cikin wasiyyarta

Dangin wata mata mai shekara 81 sun karbi diyyar fam 45,000 kwatankwacin sama da naira miliyan ashirin bayan an bar ta da rai, ba tare da amincewarta ba.

Brenda Grant ta rubuta wasiyya inda ta nuna cewa ta fi tsoron takwarkwashewar tsufa da zubewar darajarta fiye da mutuwarta bayan ta ga yadda mahaifiyarta ta zama abar tausayi sakamakon cutar mantuwa.

Sai dai asibitin George Eliot, a Nuneaton, cikin yankin Warwickshire na Ingila, ya batar da takardar inda aka rika yi mata ɗura har tsawon wata 22.

Asibitin dai tuni ya nemi afuwa saboda wannan kuskure.

Misis Grant, daga unguwar Nuneaton, ta rubuta umarnin cewa idan hankalinta ya guje ko kuma ta fuskanci wasu jerin cutuka, to bai kamata a yi mata magani ko a ci gaba da barin ta da rai ba.

Wasiyyar ta kuma tabbatar cewa bai kamata a ci gaba da ba ta abinci ba, ko da yake ana iya ba ta maganin kashe raɗaɗi idan an ga alamun darura a tare da ita.

A cikin watan Oktoban 2012, sai Misis Grant ya gamu da wani matsanancin shanyewar barin jiki da ya sanya ta gaza tafiya ko magana kai hatta ma haɗiyar abinci.

Bayan ta shafe tsawon kusan wata uku a asibitin George Eliot, sai aka sanya mata wata roba a cikinta inda ake ɗura mata abinci kai tsaye, kafin a mayar da ita zuwa gidan tsofaffi.

Image caption 'Yar Misis Grant ta ce za ta yi kokarin ganin sauran mutane ba su shiga irin taskun da mahaifiyarta ta gani ba

Wata 'yar Misis Grant, Tracy Barker ta ce tun tuni an ba wa asibitin umarni amma sai suka boye takardunta.

Lokacin da take gidan ajiye tsoffafi, sai duk ta rikice, inda ta yi kokarin cizge 'yan kwalaben da aka makala a dantsenta, abin da ya sa ma'aikatan gidan suka daura mata safar hannu.

Tracy Barker ta ce: "Tana tsoron kada a bar ta a raye, don fargabar kada a kai ta gidan tsofaffi.

"Ba ta taba kaunar ta zame wa wani wahala ba don haka ba ta son kowannenmu ya kula da ita."

Misis Grant ba ta taba fada wa danginta abin da ke kunshe cikin wasiyyarta ba, Likitanta ne ya ankarar da su jim kadan kafin a sake mayar da ita asibiti.

Yayin ganawa da jami'an asibitin, Likitanta ya tattauna tare da dangin matar, inda ya ce kamata ya yi a mutunta wasiyyarta, in ji Tracy Barker.

A ranar 4 ga watan Agustan 2014 ne aka cire wa Misis Grant kwalaben da ke ɗura mata abinci inda ta mutu bayan kwanaki kalilan.