Nigeria: An yankewa masu fyade daurin rai dai rai a Bauchi

Kungiyoyin fara hula sun sha gudanar da zanga-zanga kan karuwar aikata fyade a Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kungiyoyin fara hula sun sha gudanar da zanga-zanga kan karuwar aikata fyade a Najeriya

Wata babbar kotu a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya ta yankewa wasu mutum biyu hukuncin daurin rai da rai a gidan yari bayan samun su da laifin aikata fyade.

Kotun ta samu mutunen ne da laifin yi wa wata mace mai shekara 40 fyade tare da kwakule mata ido.

Lamarin dai ya faru ne a garin Dass a shekarar 2014.

An shafe shekara biyu ana tafka shari'ar inda alkalin kotun ta bayyana mutanen biyu a matsayin marasa imani da ya ce bai kamata suna cudanya da al'umma ba.

Jama'a da dama dai sun yi marhabin da hukuncin da suka ce zai zama darasi ga wasu da ke aikata fyade.

Matsalar aikata fyade dai matsala ce da ta zama ruwa dare a Najeriya, sai dai ba kasafai ake hukunta wadanda suka aikata laifin ba.

Kungiyoyin fararen hula sun sha gudanar da zanga-zanga kan yadda al'umma a Najeriyar ke yin wasa-rai-rai da karuwar fyade a kasar.

Labarai masu alaka