Wannan shafukan na waje ne kuma za su bude ne a wani shafin daban
Zababbun hotunan al'amuran da suka faru a Afrika da kewaye a makon nan
Hakkin mallakar hotoReutersImage caption
Wasu mutane na zaune a kusa da zanen fitaccen dan kwallon Liverpool Mohamed Salah a kofar shagon sayer da shayi a Al-kahira babban birnin Masar
Hakkin mallakar hotoAFPImage caption
Wani dan Somaliya na nuna kwarewarsa a fagen tamaula a gabar tekun Lido da ke babban birnin kasar Mogadishu.
Hakkin mallakar hotoAFPImage caption
Wasu yaran Somaliya na buga kwallo a gabar tekun Lido a Mogadishu.
Hakkin mallakar hotoReutersImage caption
Wannan yaron dan Masar hankalinsa ba a kan kwallon kafa yake ba, domin kuwa shi ya dukufa ne yana yin zikiri na mabiya darikar Sufaye.
Hakkin mallakar hotoAFPImage caption
Wata mata 'yar Sudan ta yi ado da kayan gargajiya a Madrid babban birnin Spaniya.
Hakkin mallakar hotoAFPImage caption
Wani yaro ya rufe bakinsa lokacin da yake wucewa ta wurin da masu zanga-zanga suke kona taya a Lusaka babban birnin Zambia.
Hakkin mallakar hotoAFPImage caption
Yaran Afirka ta Kudu na murnar bikin cika shekara 106 da kafa jam'iyyar ANC a kasar.
Hakkin mallakar hotoAFPImage caption
Kabilar Khoisan ma sun yi murnar cika shekara 106 da kafa jam'iyyar ANC
Hakkin mallakar hotoAFPImage caption
Kabilar Berbers da ke Arewacin Afirka na murnar sabuwar shekararsu a Ath Mendes da ke gabashin babban birnin Algeria.
Hakkin mallakar hotoAFPImage caption
Wani mutum ya saka tutar Berber ya hau doki don ci gaba da wasannin murnar sabuwar shekarar Yennayer.
Hakkin mallakar hotoAFPImage caption
Wasu 'yan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo na yin rawa da waka don nuna alhininsu a kan cika shekara 17 da kashe tsohon shugaban kasar kuma mahaifin shugaban kasar na yanzu Laurent Kabila, a babban birnin kasar Kinshasa.