Wannan shafukan na waje ne kuma za su bude ne a wani shafin daban
Hakkin mallakar hotoGetty ImagesImage caption
Shugaba Buhari ya yi alkawali ceto sauran 'yan Matan Chibok
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da 'yan matan makarantar sakandaren Dapchi su fiye da 100 a fadarsa da ke Abuja.
An gabatar wa shugaban 'yan matan ne bayan da aka bincike lafiyarsu tare da kwantar musu da hankali.
A jawabinsa lokacin ganawar, Shugaba Buhari ya ce "Ina farin cikin sanar da 'yan Najeriya da abokanmu na kasashen waje da kuma wadanda muke hada gwiwa da su cewa an sake su ne ba tare da sharadi ba.
Dalibai 107 ne dai aka sako kuma 105 daga cikinsu 'yan matan makarantar Dapchi ne da kuma mutum biyu da Boko Haram ta sace.
Shugaban ya ce sakin matan, bayan da ya umarci jami'an tsaron kasar su tabbatar babu abin da ya same su, "abin farin ciki ne."
"Na umarci dukkan jami'an tsaro da su yi aiki domin tabbatar da cewa ba mu sake ganin irin wannan lamarin ba" a cewar shugaban.
Sannan ya yi gargadi ga shugabannin hukumomin tsaro cewa da kada su kuskura a sake samun wani cikas daga bangarensu, yana mai cewa "ba zan dauki hakan da wasa ba."
Ya kuma tabbatar wa da daliban da aka kubutar cewa za su rayuwa cikin 'yanci da cimma burinsu na rayuwa a Najeriya cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da tsoron wani tashin hankali ko cin zarafi ba.
Shugaba Buhari kuma ya sha alwashin ganin an sako daliba daya da ta rage a hannun mayakan Boko Haram da kuma 'yan matan Chibok da aka sace tun 2014
Ranar Laraba aka sako 'yan matan, wadanda aka sace a watan jiya
Mahaifin daya daga cikin 'yan matan, Kundili Bukar, ya gaya wa BBC cewa wasu mutane da ake tsammani 'yan Boko Haram ne suka mayar da matan a motoci.
Abin da ya faru tun sace 'yan Matan
Hakkin mallakar hotoGGSS
A ranar 19 ga Fabrairu aka sace 'yan matan
Dalibai 110 aka sace a makarantar Dapchi
An sace su kwana daya bayan sojoji sun fice
An shiga rudani kan sace 'yan matan
Da farko an ce 'yan matan sun shiga daji ne domin buya
Sai da aka dauki tsawon mako daya kafin gwamnati ta amince an sace su
Gwamnatin Yobe ta yi ikirarin ceto 'yan matan, kafin daga baya ta nemi afuwa
Bangaren Abu Musab al-Barnawi ne ake tunanin sun sace 'yan matan
Boko Haram ba ta fito ta yi ikirarin sace 'yan matan ba
Sace 'yan Matan Dapchi ya tuna wa duniya da 'yan matan Chibok
Wannan ya nuna har yanzu Boko Haram barazana ce
A cewarsa, sun ajiye su ne kawai suka tafi kuma 'yan matan sun nuna alamar matukar gajiya.
Jam'iyyar PDP mai hamayya a Najeriya ta yi zargin cewa jam'iyyar APC da fadar shugaban kasar ne suka kitsa sace matan domin cimma wata bukata ta siyasa.
Sai dai APC ta musanta zargin.
A watan jiya aka sace matan, lamarin da ya janyo mummunar suka kan gwamnati da jami'an tsaron Najeriya.
A wancan lokacin, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana sace 'yan matan a matsayin wani bala'i da ya shafi kasar baki daya.
An samu sa'insa tsakanin Sojoji da 'Yan sanda kan wadanda alhakin tsaron Dapchi ya rataya a kan wuyansu, inda 'yan sanda suka ce ba da saninsu sojoji suka fice ba.
Kafar yada labarai ta Amurka ta Wall Street Journal, WSJ, ta ce ta samu bayanan da suka tabbatar mata da cewa bangaren Abu Musab Abu Musab al-Barnawi ne suka sace 'yan matan 110.
Amnesty International ta zargi sojojin Najeriya da yin biris da gargadin cewa 'yan Boko Haram za su kai hari sa'o'i kalilan gabannin a sace 'yan matan sakandaren Dapchi sama da 100, zargin da sojojin suka musanta.