Fyade da kisan yarinya Musulma ya ta da rikici a Indiya

Asifa Bano Hakkin mallakar hoto Courtesy family of Asifa Bano
Image caption Shekarar Asifa Bano takwas lokacin da aka kashe ta

Fyade da kuma kisan da wani gungun maza suka yi wa wata yarinya mai shekara takwas a Kashmir da ke karkashin ikon Indiya ya janyo zaman dar-dar a yankin.

Da safiyar ranar 17 ga watan Janairu, Muhammad Yusuf Pujwala na zaune a wajen gidansa da ke Kathau, lokacin da daya daga cikin makwabbtansa ya zo da gudu ya fada masa cewa an gano gawar 'yarsa mai shekara 8, Asifa Bano.

An ajiye gawarta a cikin daji a wani wuri mai nisan kilomita dari.

"Na san wani abu marar kyau ya faru da ita," a cewar Mista Pujwala mai shekara 52 a hirar da ya yi da BBC.

Matarsa, Naseema Bibi na zaune kusa da shi tana kuka, tana kiran sunan ''Asifa".

Mista Pujwala 'na cikin al'ummar makiyaya musulmi da ake kira Gujjars ne wadanda suke tafiya a yankin Himalayas da akuyoyinsu da kuma baunarsu.

Al'amarin ya tayar da hankula sosai, kuma ya fito da abin da yake hadassa rikici tsakanin mabiya Hindu ma su rinyaje da ke Jammu da kuma musulmi masu rinjaye a Kashmir yankin da ke fama da rikici.

'Yan sanda sun kama mutane takwas, ciki har da wani jami'in gwamnati da ya yi ritaya daga aiki, da wasu jami'an 'yan sanda hudu da kuma wani matashi da shekarunsa ba su kai 18 ba wadanda ake zagin suna da hannu a kisan Asifa.

Sai dai kamen ya janyo zanga-zanga a Jammu, kuma ministoci biyu daga jam'iyyar BJP ta mabiya addinin Hindu sun halarci gangamin nuna goyon bayan da aka yi wa wadanda ake zargi.

Jamiyyar BJP ce ta ke mulki a jihar tare da hadin gwiwar jam'iyyar Peoples Democratic Party( PDP ) .

Shin ya aka yi Asifa ta bata?

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kisan ya fito da abubuwan da ke kawo matsala a jihar da ke fama da rarabuwar kawuna

A lokacin da ta bata a ranar 10 ga watan Janairu, iyalinta na zama ne a wani kauye mai nisan kilomita 72 da garin Jammu.

Mahaifiyarta ta ce a wannan ranar Asifa ta je daji ne domin ta dawo da dawakai gida, amma sai aka ga dawakan sun dawo ba tare da Asifa ba.

Naseema ta fadawa mijinta abin da ya faru, sai shi da wasu makwabtansa suka fara nemanta a cikin daji amma ba su ganta ba.

Bayan kwana biyu da aukuwar lamarin, sai iyalinta suka shigar da kara a gaban hukumar 'yan sanda.

Amma a cewar Mista Pujwala, 'yan sandan ba su taimaka ma su ba, inda ya yi zargin cewa daya daga cikin 'yan sandan ya fada ma sa cewa Asifa "ta gudu ne" tare da wani saurayi.

Sai dai yayin da wannan mummunan labarin ya bazu, al'ummar Gujjar sun yi zanga-zanga kuma inda suka datse wata babbar hanya da motoci suke bi, abin da ya tilastatwa 'yan sanda tura jami'ansu biyu zuwa wurin da ake neman Asifa.

Deepak Khajuria na cikin jami'an 'yan sanda da aka tura amma daga bisani an kama shi saboda ana zargin yana da hannu a cikin kisan.

Bayan kwanaki biyar aka gano gawar Asifa.

"An gallaza ma ta, an karya kafufuwanta" a cewar mahaifiyarta Naseema.

Shin menene masu bincike suke ganin ya faru?

Bayan kwanaki shida da gano gawar Asifa, gwamnan jihar Jammu da Kashmir, Mehbooba Mufti ya ba da umurnin gudanar da bincike kan lamarin.

A cewar masu biciken, an kulle Asifa a wurin ibada na mabiya hindu har na tsawon kwanaki kuma an rika ba ta maganin da ya sa ta fita daga cikin hayyacinta.

Rahoton masu binciken ya yi zargin cewa an rika yi ma ta "fyade har tsawon wasu kwanaki," tare da gallaza ma ta kafin daga bisani aka kashe ta."

An kashe ta ne ta hanyar shakewa, kuma an buge ta a "ka" har sau biyu da dutse.

Sanji Ram, mai shekara 60, wanda tsohon ma'aikacin gwamnati ne, na cikin wadanda ake tuhuma da shirya kisan tare da taimakon wasu jami'an 'yan sanda.

Hakkin mallakar hoto Sameer Yasir
Image caption Lauyoyi a Jammu sun yi kokarin hana 'yan sanda shiga cikin kotu domin su shigar da kara

Ana kuma zargin dan Mista Ram da wani dan uwansa da abokinsa da kuma wani matashi da shekarunsu ba su kai 18 da yin fyade da kuma kisa.

Masu binciken sun yi zargin cewa Mista Khajurai da jami'an 'yan sanda suke cikin tawagar da suka rika neman Asifa, sun wanke tufafin Asifar da suka yi jina-jina kafin suka tura su dakin da ake binciken kwa-kwaf.

Sun yi ammanar cewa wadanda ake zargi suna son su firgitar da al'ummar Gujjar domin su bar garin Jammu.

Makiyayan na amfani da filin jama'a da kuma daji da ke Jammu domin yin kiwo kuma dabbobinsu su ci abinci, lamarin da janyo tashe-tashen hankula tsakaninsu da wasu mazauna mabiya addinin Hindu da ke yankin.

"Abu ne da ya shafi fili," a cewar Talib Hussain, mai fafitukar kare hakkin kabilu kuma lauya.

Mista Hussain, wanda shi ne ya jagoranci zanga-zangar da aka yi domin nuna goyon baya ga iyalin Asifa, ya yi zargin cewa 'yan sandan karamar hukuma sun kama shi kuma sun yi ma sa barazana.

Ankur Sharma, wanda yana cikin lauyoyin da suka yi zanga-zangar goyon bayan mutanen da ake tuhuma, ya yi zargin cewa musulmi makiyaya na kokarin sauya yawan al'ummar Jammu inda mabiya Hindu suka fi rinjaye.

"Suna keta haddin dajinmu da kuma albarkatun ruwan sha," kamar yadda ya shaidawa BBC.

Sai dai yayin da kisan bai ja hankalin mutane sosai ba a Jammu, amma jaridu a Srinagar babban birnin Kashmir sun buga labarin a gaban shafukan jaridunsu.

Shin mene ne ya faru a jana'izar Asifa?

Kabilar Gujjars makiyaya sun so su a binne Asifa a cikin makabartar da suka saye fili a cikin shekarun da suka gabata inda suka binne mutane biyar.

Sai dai lokacin da suka iso wurin, Mista Pujwala ya ce masu tsattsauran ra'yin adinin Hindu sun yi barazanar ta da da zaune-tsaye idan suka ci gaba da jana'izar.

"Sai da muka yi tattakin mil bakwai domin mu binne ta a wani kauye," a cewar Mista Pujwala.

Ya rasa 'ya'yansa mata biyu a cikin wani hadari, bayan da matarsa ta nace, ya dauki Asifa a matsayin 'yar reno daga wurin surukinsa.

Matarsa ta bayyana Asifa a matsayin yarinya mai 'kazar-kazar', Idan sun yi tafiya ita ce take kula da awakai.

Labarai masu alaka