Commonwealth: Abubuwa 7 da baku sani ba kan kungiyar

Sauraniya Elizabeth a Indya a 1997 Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Shugabar kungiyar kasashe renon Ingila Commonwealth a taron kungiyar a Indiya a 1997.

Shugabannin kungiyar Common wealth na taro a Landan.

Ga wasu abubuwa bakwai da watakila ba ku sani ba kan wadannan kasashe.

1) Kashi daya cikin uku na mutanen duniya suna kasashen Commonwealth

Kusan mutane biliyan 2.4 daga cikin biliyan 7.4 na al'ummar duniya baki daya, na zaune a kasashen 53 da ke kungiyar Commonwealth.

Kuma akasarin su shekarunsu ba su haura 30 ba.

Kasar da ta fi yawan al'umma ita ce Indiya, sai dai akwai kasashe 31 daga cikin kungiyar wadanda yawan al'umarsu ya kai miliyan 1.5 ko kuma kasa da haka.

2)Wasu mambobin basa cikin daular Birtaniya.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jamus da Belgium ne suka yi mulkin mallaka a Rwanda ba Ingila ba

A shekarar 2009 da 1995 ne Rwanda da Mozambique suka zama 'ya'yan kungiyar, kuma dukkansu ba su da wata alaka da mulkin mallaka na Birtaniya.

Sai dai a baya akawai wasu kasashe da suka fice daga cikin kungiyar.

Robert Mugabe ya fitar da kasarsa Zimbabwe a shekarar 2003 bayan dakatar da kasar daga cikin kungiyar saboda rahotanin da suka yi zargin cewa an yi magudi a lokacin zabe.

A shekarar 1999 ne aka dakatar da Pakistan bayan juyin mulkin soja amma ta sake komawa cikin kungiyar bayan shekara hudu da rabi.

Kasar Afrika ta kudu ta fice daga kasar ashekarar 1961 bayan da mambobin Commonealth suka soki manufofin kasar kan wariyar launin fata, Sai dai ta sake komawa kungiyar a shekarar 1994.

Sai kuma Maldives wadda ta fice a shekarar 2016 .

3) Sarauniya Elizabeth ita ce shugabar kasa a kasashe 16 na kungiyar

Akasarin kasashe jamhuriya ne kuma shida da ga ciki, Lesotho da Swaziland da Brunei da Darrsusalam da Malaysia da Samoa da Tonga na da sarakunansu.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tonga na da sarkina kanta - Sarki Tupou VI (tskiya)

4) Wuri ne mai fadi

Kungiyar ta mallaki kusan kashi daya bisa hudu na doron kasa.

Mafi girman fadin kasa daga cikinsu ita ce Kanada, wadda ita ce kasa ta biyu mai karfin tattalin arziki a duniya.

Indiya da Austreliya suma suna da fadi sosai.

Sai dai akwai kananan kasashe irinsu tsibirin Nauru da Samoa, daTuvalu da Vanuatu, da Dominica da Antigua da Barbuda wadanda suke yankin Karebiya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tsibirin Nauru

5) Ta sauya sunanta

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugabannin kungiyar Commonwealth sun yi taro a Landan a shekarar 1969

A shekarar 1949 aka kafa kungiyar bayan da aka cire sunan Birtaniya kuma aka cire yi wa masarautar Ingila mubaya'a da ga cikin manufofin kungiyar.

Mutune biyu ne kawai suka taba rike mukamin shugabancin kungiyar, Sarki George na shida da Sarauniya Elizabeth ta biyu.

Duk da cewwa ba gadon mukamin ake ba, amma ana tsammanin cewa Yerima Wales mai jiran gadon Sarautar Ingila shi ne zai gaji mukamin idan ya zama sarki.

Kasashen da suka kafa kungiyar ta Commonwealth sun hada da Austreliya da Kanada, da Indiya, da New Zealand, da Pakistan, da Afrika ta kudu da Sri Lanka da kuma Birtaniya.

A wancan lokaci kungiyar ba ta da kundin tsarin mulki, sai daga bisani a shekarar 2012 inda ta nemi mambobinta su bi manufofinta 16,

Manufofin sun har da bin tafarkin mulkin dimukradiya, da daidato tsakanin mata da maza, da samun ci gaba mai dorewa, da kuma zaman lafiya da tsaro a kasashen duniya.

An dai rika sukar kungiyar a matsyin wani gungun kasashen da Birtaniya ta mallaka bayan kuma kungiyar ba ta da wani tasiri.

A shekarar 2013 Gambiya ta fice daga kungiyar inda ta bayanna ta a matsayin wata cibiyar turawa musu son ci ga da mulkin mallaka.

Magoya bayan kungiyar sun ce alfanun da ake samu daga kungiyar sun hada da zama mamba da nuna goyon baya wajan samar da ci gaba da kuma hadin kan kassahe wajen cimma muradun duniya.

Sakatariyar kungiyar Lady Scotland, ta ce: " Mambobinmu suna aniyar ganin cewa sun raya kuma sun kare mulkin dimukradiyya da kuma tabbatar da ci gaban rayuwa tare da mutunta yancin kowa da kowa."

6) Birtaniya ita ce ke da tattalin arzikin mafi karfi a kungiyar Commonwealth

Indiya za ta iya zama ta daya nan ba da jimawa ba, watakila a farkon badi.

Idan aka hada ma'aunin arzikin kasashen su 53 baki daya ke samarwa ya kai dala triliyan 10. kusan karfin tattalin arzikin cikin gida da China ta ke samarwa watau dala triliyan 11.

Sai dai arzikin bai kai wanda Amurka ta samarwa ba wata dala triliyan 19 .

7) Akwai wata kungiya kuma banda Commonwealth

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A baya bayan shugabannin Kungiyar kassahen renion tsohuwat tarayyar Soviet suka yi taro a birnin Minsk, na kasar Belarus

Akwai kungiyar renon Faransa watau La Francophonie masu amfani da harshen Farasanci.

Akwai kuma kungiyar Commonwealth masu 'yanci wadanda tsoffafin kasashen tarayyar Soviet suka kafa a shekarar 1991 .