Bishiya ta kashe daliban Najeriya uku a Kamaru

bishiya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lamarin ya faru ne bayan daliban tare da wasu takwarorinsu suka nemi fakewa a karkashin wani tanti a lokacin da ruwan sama yake sauka

Wata bishiya ta yi sanadiyyar mutuwar wasu dalibai uku 'yan asalin Najeriya a yayin da wasu 16 kuma suka ji rauni a Jamhuriyyar Kamaru.

Wannan lamarin ya faru ne a gidan ajiye namun daji na Bouba Ndjidda da ke arewacin Kamaru, bayan wata guguwa da kuma iska mai karfi sun kayar da bishiyar sanadiyyar saukar ruwan sama.

Wata sanarwar da Gwamnan Lardin Arewa Jean Abate Edi'i ya fitar, ta tabbata da rasuwar daliban uku 'yan asalin Najeriya a gidan ajiye namun dajin.

Lamarin ya faru ne bayan daliban tare da wasu takwarorinsu sun nemi fakewa a karkashin wani tanti a lokacin da ruwan saman ya sauka.

Wata guguwa da ta rinka kadawa ta kai ga tumbuke wata bishiya ta yi jifa da ita a kan tantin da wadannan dalibai suka fake.

A nan take uku daga cikinsu suka mutu, yayin da wasu 16 kuma suka ji rauni.

Tuni sanarwar ta Gwamnan ta kara da cewa a take aka aika wani jirgi ya kwaso wadanda suka ji rauni da kuma gawawwakin wadanda suka mutu aka kai su asibitin birnin Garoua, inda a yanzu haka aka ajiye gawawwakin kuma ana kula da wadanda suka ji raunin.

Baya ga haka kuma Gwamnan ya bayar da umurnin kwashe sauran daliban da suke gidan ajiye namun dajin da kuma malaman da suke horar da su, a maida su Garoua.

Rahotanni sun ce a ranar 13 ga watan Afrilun nan ne wasu dalibai 50 na jami'ar jihar Taraba a arewacin Najeriya tare da malamansu shida suka kai wata ziyarar bincike a gidan ajiye namun dajin na Bouba Ndjidda da ke garin Rey-Bouba, inda wasu suka gamu da ajalin nasu a can.

Labarai masu alaka