Nigeria: An gano sandar Majalisa da aka sace

An gano sandar ne a wani wuri dake kusan da kan gadar kofar gari wato City Gate da ke Abuja. Hakkin mallakar hoto Senate
Image caption An gano sandar ne a wani wuri dake kusan da kan gadar kofar gari wato City Gate da ke Abuja.

Rundunar 'yan sandan Nigeria ta ce an gano sandar girmar Majalisar da wasu 'yan daba suka sace.

Haka kuma rundunar ta ce an tsauran matakan tsaro a ciki da wajen Majalisar dokokin tarayya.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da mataimakin jami'in hulda da jama'a ta rundunar SP Aremu Adeniran ya aikewa manema labaru.

Sanarwar ta ce an gano sandar ne a wani wuri dake kusan da kan gadar kofar gari wato City Gate da ke Abuja.

Rundunar ta kara da cewa wadanda suka sace sandar sun jefar da ita ne sakamakon tsaurara tsaro da 'yan sanda suka yi a Abuja.

Hakan na zuwa ne bayan da Mataimakin shugaban Nigeria Farfesa Yemi Osibanjo ya gana da mataimakin shugaban Majalisar dattawan kasar Sanata Ike Ekweramadu.

Ganawar dai ta biyo bayan kutsawa cikin zauren majalisar da wasu suka yi a daidai lokacin da Majalisar ke zama a Jiya Laraba, inda suka haddasa rudani a zauren majalisar kana kuma suka yi awon gaba da sandar girma ta majalisar.

Sanata Ike Ekweramadu ya shaidawa manema labaru cewa ya je fadar gwamnatin ne don yiwa mataimakin shugaban kasar karin bayani kan abun daya faru a Majalisar.

Mece ce Sandar Majalisa?

  • Sandar Majalisa da ake kira 'Mace' ta sha bamban da sauran alamun majalisar
  • Sandar tana da matukar muhimmancin gaske, inda majalisa ba za ta taba zama ba sai da ita
  • Sandar ita ce alamar iko a dukkan majalisun dokokin kasar na tarayya da na jihohi
  • Ana tafiya da Sandar a gaban shugaban majalisa a duk lokacin da zai shiga ko fita daga majalisar
  • Wani Sajan na Majalisar ne yake da alhakin daukarta a kafadarsa ta dama.