Firai ministar Birtaniya ta shawarci Najeriya ta halasta luwadi

Firaministar Birtaniya, Theresa May Hakkin mallakar hoto Getty Images

Firai ministar Birtaniya, Theresa May, ta bukaci dukkan kasashen da ke karkashin kungiyar Commonwealth da su sake tunani a kan dokar auren jinsi.

Misis May, ta sanar da hakan ne a birnin Landan, a lokacin da take bayani a wajen taron kungiyar ta Commonwealth.

A shekarar 2014 tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sa hannu a kan kudurin dokar da ta haramta auren jinsi guda; watanni kadan bayan nan kuma aka fara aiki da dokar bayan Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da ita.

A karkashin dokar, duk wanda kotu ta samu da laifin duk wata hulda ta luwadi ko madigo ko auren jinsi guda ko zaman dadiro a tsakanin jinsi guda, to za a daure shi shekara 14 a gidan yari.

Sai dai Firai Ministar Burtaniya ta tsaya a kan cewa bai kamata wani ya ayyana wata doka da za ta takura wa wani ko ta nuna wariya a gare shi ba saboda irin mutanen da ya zabi ya yi soyayya da su.

Misis May ta ce Burtaniya za ta goyi bayan duk wata kasa da ke a shirye ta soke dokokinta da suka haramta auren jinsi guda.

Firai ministar ta ci gaba da cewa, "yanzu duniya ta sauya daga abubuwan da suka faru shekara 50 da ta wuce, inda ake tsarawa mutane yadda za su tafiyar da rayuwarsu."

Ta ce yanzu matasa suke tsara yadda za su tafiyar da rayuwar da suke so.

Theresa May, ta ce a taron karshe da shugabannin kungiyar ta Commonwealth suka yi, an amince za a samar da wata hukuma da za ta rinka tallafawa 'yan madigo da luwadi da kuma 'yan daudu.

Masu lura da al'amura dai na ganin kafin kungiyar kasashen Commonwealth ta ci gaba da wanzuwa, wajibi ne a cika alkawuran da aka dauka a zahiri ba kawai a fatar baka ba a tsawon kwanaki biyu da shugabannin za su shafe suna wannan taron.

A baya dai wasu manyan kasashen Commonwealth kan tura mukarraban gwamnati ne don halartar taron da ake shirya wa.

Sai dai a wannan karon kusan daukacin shugabannin kasashen da Firai ministoci ne da kansu za su saurari jawabin sarauniyar a fadar, wanda ake hasashen cew shi ne jawabi na karshe da za ta gudanar a taron Commonwealth, ganin halin lafiyarta da kuma yadda ake daukar tsawon lokaci ba a yi taron ba.