Wajan yawon shakatawa da masu laken asirin Israila suka bude

Image caption Hoton Gad Shimron a wurin yawon bude ido na Arous

Arous wurin yawon bude ido ne da ke bakin tekun Maliya da ke cikin hamadar .

Sai dai wannan wuri mai ban sha'wa , ya kasance wani sansani na jami'an leken asirin Isra'ila, wadanda aka turosu domin yin aiki na musamman.

A cikin hotunan da aka wallafa an nuna kananan gidaje da aka gina kusa da bakin teku ,inda aka nuna wasu ma'aurata sanye da kayan ninkaya suna murmushi , akwai kuma kifaye iri -iri , kuma ruwan tekun na cikin ruwan teku mafi ya kyau a duniya.

An dai wallafa dubban kananan takardu da aka raba wa masu kula da harkokin tafiye-tafiye na musaman a turai.

An bude wani ofishi a birnin Geneva inda masu aniyar yin tafiyar yawon bude ido ke zuwa wurin su zabi rana da kuma lokacin da zasu yi tafiya.

Daga bisani kuma an samu daruruwan baki da suka rika zuwa hutu daga wannan wuri.

Hukumar kula da masu yawon bude ido ta Sudan ta yi farin ciki da aka bude wannan waje.

Ta bayar da hayar wajen ne ga wasu mutane da suka ce su 'yan kasuwa ne daga kasashen turai, wadanda suka yi sanadin kawo masu yawon bude ido daga kasashen waje na farko zuwa kasar.

Sai dai abinda baki da kuma hukumomi basu sani ba, shi ne cewa wurin yawon shakatawa da ke bakin tekun Maliya na bogi ne.

Wuri ne da jami'an leken asirin Isra'ila wato Mossad, suka bude kuma sun yi fiye da shekara hudu suna tafiyar da harkokinsu a farkon shekarun 1980.

Sun rika amfani da wurin ta bayan fage a matsayin wurin gudanar da ayyukan jinkai - domin ceto dubban yahudawa 'yan Habasha da suka makale a cikin sansanonin Sudan, inda suke kwashesu domin su mai da su Israila.

Sudan dai kasar Larabawa ce da bata kaunar Isra'ila, a kan haka aikine da aka yi, ba tare da sanin kowa ba.

"Aikin sirri ne, ba bu wani da ya yi magana akansa ,"a cewar Gad Shimron, daya daga cikin jami'an leken asiri da suka yi aiki a cikin kauye. " Ko iyalina ba su san da maganar ba ."

Hakkin mallakar hoto Gad-Shimron
Image caption Gad yana cikin jirgin ruwan roba da ake hura wa iska a wani wuri kusa da kauyen Arous

Yahudawa 'yan Habasha sun fito daga cikin wata al'umma da ake kira Beta Israel ( gidan Israila), wadanda ba a tabbatar da asalinsu ba.

Wasu sun yi ammanar cewa suna da dangantaka da kabilu 10 da suka bata a masarautar Israila wadanda suka yi wa dan sarauniya Sheba da kuma sarki Solomon rakiya zuwa Habasha a shekarar 950 kafin wanzuwar Annabi Isa.

Wasu na ganin sun gudu ne bayan da aka lalata wurin ibada na yahudawa a shekarar 586 kafin wanzuwar Annabi Isa.

Sun rika amfani da litafin Torah kuma sun rika addu'oi a wuraren ibada na yahudawa, sai dai sun shafe shekaru aru- aru basu yi mu'amala da 'yan uwansu yahudawa ba, sun yi amanna cewa su ne yahudawan karshe da suka rage a duniya.

Sai dai manyan limaman yahudawa sun tabbatar da sahihancin yahudawa 'yan kabilar Beta a farkon shekarun 1970.

A 1977, daya daga cikin mambobinsu , Ferede Aklum, ya shiga cikin wasu 'yan gudun hijira 'yan Habasha wadanda ba yahudwa bane da suka tsallaka iyaka zuwa Sudan domin tsere wa yakin basasa da kuma matsalar karancin abincin da ake fuskanta.

Hakkin mallakar hoto AAEJ Archives Online
Image caption Ferede Aklum (ta hagu ) da kuma jagoran yahudawa yan Habasha Baruch Tegegne

Ya aikewa cibiyoyin jin kai da wasika , inda ya rika neman taimakonsu, kuma daya daga cikin wasikunsa ta fada hannun hukumar leken asirin Israilar watau Mossad.

Fira ministan Israila na wancan lokaci , Menachem Begin - wanda shi ma dan gudun hijira ne a lokacin da 'yan Nazi suka mamaye turai- ya ce an kafa Israila ce domin ta kasance tudun mun tsira ga yahudawan da suka bazu a duniya, kuma ya umuurci hukumar a kan ta dauki mataki.

A wannan lokaci yahudawa Beta dubu 14,000 suka yi tattaki mai nisan km800 tare da wasu 'yan Habasha fiye da miliyan da suke neman mafaka a iyakar Sudan .

Hakkin mallakar hoto AAEJ Archives Online
Image caption Yahudawan Habasha a Sudan , 1983

Yahudawa 'yan gudun hijira 1,500 suka hallaka lokacin da suke kan hanya ko kuma suka bata a cikin sansanonin da ke Gedaref da kuma Kassala, ko kuma aka yi awon gaba dasu .

Image caption Wasu yahudawan Habasha a cikin jirgin ruwa

Aikin ceto yahudawan Habasha

Ba tare da bata lokaci ba , aka fara ayyukan ceto yahudawan Habasha, inda wasu suka fice daga Sudan domin zuwa turai zuwa Isra'ila, amma sun yi amfani da takardun tafiye- tafiye na bogi.

"Mun nemi taimakon wani jirgin ruwan yaki na Israila", a cewar wani babban jami'i da aka yi aikin da shi wanda ya nemi a sakaya sunansa.

" suka ce toh , kuma daga nan wasu jami'an Mossad suka je Sudan domin neman bakin teku da za a iya amfani da shi.

Sai suka gano wani kauye da ba bu kowa da ke bakin teku .

Wurin yawon bude ido na bogi

Sun shafe shekara guda suna akin gyara wurin kuma sun cimma matsaya da wasu 'yan kasar a kan su rika samar musu da ruwan sha da kuma man fetur.

Sun kuma dauki ma'aikata 15 ciki har da masu shara da goge-goge da direba da kuma mai girki daga wani otel.

"Mun ninka masa abinda ake biyansa a wurin da ya yi aiki a baya" a cewar jami'in da baya son a bayyana sunansa.

Ba bu wani daga cikin ma'aikatan da ya san dalilin da yasa aka kafa wurin yawon bude ido ko kuma farar fata da suke aiki tare da su, jami'an leken asirin Israila.

Hakkin mallakar hoto Gad Shimron
Image caption Gad da wani dan Israila a cikin motar kwashe kaya a Sudan

Daga wannan wurin ne tawagar manyan motocin masu dauke da yan gudun hijira ta yi tafiyar yini biyu , inda ta rika kaucewa wuraren gudanar da bincike ta hanyar bada toshiyar baki ko kuma wuce su da karfin tsiya.

Idan sun tsaya domin su huta, suna kokarin kwantar da hanklin fasinjojin da suka tsorata.

Idan sun iso bakin teku da ke arewacin kauyen yawon bude ido, sojojin Israila za su zo bakin teku da jirgen ruwan roba da ake hura wa iska domin su kwashe 'yan gudun hijira inda zasu sake yin tafiyar awa daya da rabi zuwa wani babban jirgin ruwan yaki da ake kira, INS Bat Galim.

Jirgin kuma zai wuce da su zuwa Israila.

Image caption Wasu yahudawa Habasha na cikin jirgin ruwa da ya kwashe su daga bakin teku domin ya kai su jirgin ruwa yaki

"Aiki ne mai hadari sosai ," a cewar jami'in da be amince a bayanna sunansa ba. " Mun san cewa idan aka capke mu toh mun san kashemu za a yi ta hanyar rataya a Khartoum."

Sai dai saura kiris da an kamasu a watan Maris na shekarar 1982, lokacin da sojojin Sudan suka hango wani ayari da ke dauke da 'yan gudun hijira a bakin teku.

Watakila sun dauka masu safarar mutane ne inda suka rika harbin gargadi, sai dai sojojin Isra'ilan, sun samu wucewa da 'yan Habashan da ke cikin jirgin.

Bayan wannan lamarin ne aka yanke shwarar cewa akwai hadari a aikin kwashe mutane a cikin jragen ruwan yaki kuma aka bullo da wani tsarin.

An dora wa jami'an leken asirin alhakin nemo fili a cikin hamada da jiragen sama samfurin C130 Hercules zasu iya sauka..

Za a kwashe 'yan gudun hijira da jirgin sama cikin sirri .

Jigilar kwashe yahudawan Habasha a cikin jirgi.

An dai rika jigilar kwashe 'yan gudun hijirar a cikin jiragen sama .

Gad da kuma tawagarsa, sun samu wani sako da ya ce akwai wani fiin da Birtaniya ta yi amfani da shi a yakin duniya na biyu da ke kusa da gabar teku. kuma a watan Mayu na shekarar 1982 jirgin sama samfurin Hercules, da ke dauke sojojni Israila ya sauka da tsakar dare.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jirgin saman Israila samfurin C130 Hercules

A cikin jerin jigilar jiragen sama da aka yi har sau 28 da wani jirgin kamfanin wasu yahudawa dake Belguim, an kwashe yahudawan Habasha dubu 6,380 zuwa Brussels, daga nan kuma aka wuce da su zuwa Israila.

An yi wa aikin lakabi da Operation Moses.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu yahudawa Habasha a cikin jirgin saman yakin Israila da ya tashi daga Addis Ababa a 1991

An fasa kwai

Jarindu a sassa daban-daban na duniya, sun wallafa labarin a ranar 5 ga watan janairu na shekarar 1985, kuma Sudan ta dakatar da aikin jigilar ba ta tare da bata lokaci ba.

Ta kuma musanta zargin da ake yi cewa ta hada kai da Israila inda ta ce wani shiri ne da "Israila da Habasha suka kitsa"

Sai dai a ranar 6 ga watan Afrilu na shekarar 1985, aka kifar da gwamnatin janar Nimeiri sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi .

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Janar Nimeiri

Sabuwar gwamnatin sojin ta mai da hankali ne wajan daukar matakin korar jami'an leken asirin Israila, domin ta karfafa kimarta a idanun kasasahen Larabawa.

Shugaban hukumar leken asirin Isra'ila ya kuma bada umarnin barin wurin yawon shakatawar.

Labarai masu alaka