An dakatar da farfesa saboda 'yunkurin lalata' da daliba

Ana yawan samun dalibai da ke zargin cewa malamansu sun nemi yin lalata da su Hakkin mallakar hoto OAU
Image caption Kawu yanzu malamin da ake zargi bai ce komai ba

Jami'ar ta Obafemi Awolowo ta ce an dakatar da farfesan ne bayan tabbatar da cewa muryar da aka nada ta malamin ce da ya nemi yin lalata da dalibarsa.

Mr. Abiodun Olanrewaju, babban jami'in hulda da jama'a na jami'ar ya fadawa BBC cewa an dakatar da farfesan har zuwa lokacin da za a kammala bincike kan zargin.

"Shugaban jami'ar Obafemi Awolowo ya karbi rahoton farko da aka gabatar bayan fara gudanar da bincike, kan wadda ake zargi da neman yin lalata da wata dalibar makarntar", In ji Abiodun.

Farfesa Richard Akindele na koyarwa ne a sashin harkokin kasuwanci da hada-hadar kudi na jami'ar ta OAU.

An kuma gano cewa muryar da aka nada da waya ta wata daliba ce Monica Osagie da ake zargi farfesan ya yi yunkurin yin lalata da ita domin ya kara mata maki.

Duk da cewa kwamitin da ke gudanar da binciken ya gayyaci mutanen biyu, to amma farfesa Akindele ne ka dai ya gurfana.

Jam'iar ta ce Monica ba ta halarci gayyatar da kwamitin ya yi mata ba, sannan ba ta tura da wakilci ko wani uzuri ba

A yanzu kwamitin na jiran Osagie ta gurfana a gabansa domin bayar da na ta bahasin, kafin a fitar da rahoton karshe.

Matukar an same shi da laifin yunkurin yin lalata da dalibar, to farfesa Richard Akindele zai iya fuskantar kora daga jami'ar ta Obafemi Awolowo.

Cin zarafi ta hanyar lalata laifi ne a Najeriya, amma duk da haka ana ci gaba da samun aukuwar lamura irin wannan a jami'oin Najeriya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana yawan samun dalibai da ke zargin cewa malamansu sun nemi yin lalata da su

Labarai masu alaka