Yadda za a magance matsalar yoyon fitsari
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda za a magance matsalar yoyon fitsari

Yoyon fitsari babbar matsala ce da ke shafar mata yawanci a Afrika.

Mata na samun matsalar ne bayan haihuwa.

Doguwar nakuda da auren-wuri da talauci na daga cikin matsalolin da ke haifar da yoyon fitsari.

Matan da matsalar ta shafa yawanci suna fuskantar kyama daga mazajensu da kuma jama'a saboda warin da ke fitowa daga jikinsu sakamakon matsalar ta yoyon fitsari.

Amma ana iya magance wannan matsalar idan al'umma ta sauya yadda ta dauki mata musamman ta fuskar wadatar da su da abinci mai gina jiki da kuma jinkirta daukar cikin fari.

Haka kuma samar da cibiyoyin kula da matsalar zai taimaka wajen kawo karshen lalurar.

Masu fama da matsalar na matukar bukatar taimako da fahimta daga mazajensu da kuma al'umma domin samun lafiyarsu.

Shirin a wannan makon ya tattauna ne da liktar mata Dr Zainab Dattti Ahmad kan dalilan da ke janyo cutar da kuma yadda za a tunkare ta.