Gobara ta kama ofishin hukumar zaben jihar Kaduna

Gobarar ta shafi muhimman sassa a hukumar zaben jihar Kaduna Hakkin mallakar hoto Muhammad Ibrahim
Image caption Gobarar ta shafi muhimman sassa a hukumar zaben jihar Kaduna

Gobara ta tashi a ofishin Hukumar zabe ta jihar Kaduna da safiyar ranar Asabar, inda ta yi mummunan ta'adi.

Babu wanda ya mutu ko ya jikkata a gobarar, to amma Shugabar hukumar Saratu Binta Dikko tace gobarar ta shafi gaba daya ofisoshi a hawa na biyu.

"Gobarar ta shafi dukkanin ofisoshi a hawa na biyu, da suka hadar da ofishin shugaban hukumar, da sashin shari'a da sashin kudi, da dakin taro." Inji Shugabar.

To amma ba abinda ya shafi hawa na daya da kuma ofisoshin da ke kasa.

Har kawo yanzu dai ba a bayyana dalilin gobarar ba, amma Saratu Binta Dikko ta shedawa manema labarai cewa ce tuni 'yan kwana-kwana da 'yan sanda suka kaddamar da bincike.

To sai dai shugabar hukumar zaben ta ki amsa tambayoyoin manema labarai bayan jawabin da ta yi musu.

Gobarar ta tashi ne a dai dai lokaacin da ma'aikatan hukumar ke wata ganawar gaggawa a ofishin shugaban hukumar, wanda shi ma ya kone.

Sharhi

Gobarar ta tashi ne kasa da wata daya kafin gudanar da zaben kananan hukumomin jihar, da aka tsara ranar 12 ga watan gobe.

Wannan ka iya kasancewa wani koma baya ga zaben, wanda wasu suka dade suna bukatar gwamnatin jahar ta gudanar.

Akwai dai masu ganin gwamnatin na dari-dari wajen gudanar da zaben, wanda wasu suke dauka a matsayin ma'aunin karbuwar gwamnatin jihar ko akasin haka a wajen jama'a.

A bara gwamnatin ta kori dubban ma'aikata musamman malaman makarantar primary da ma'aikatan kananan hukumomi

Gwamnatin ta ce malama ba su cancanci koyarwa ba, sannan ma'aikatan kananan hukumomi kuma sun wuce yadda ake bukatarsu.

Ko da zaben fidda gwani na 'yan takarar shugabannin kananan hukumomi da na kansiloli na APC na cike da cece kuce, inda wasu ke zargin gwamnatin jahar da yin karfa-karfa.

To amma gwamna Malam Nasir El-Rufai ya ce ba shi da dan takara, kuma kowa nasa ne.

Gwamnatin ta jihar Kaduna na son yin amfani da na'ura wajen gudanar da zaben.

Kuma ko da ya ke shugabar hukumar zaben Saratu Binta ta ce gobarar ba ta shafi dakin ajiye kayayyakin hukumar ba, sai dai ta ce za a dauki wasu kwanaki kafin a gama gano irin barnar da gobarar ta yi.

Don haka a yanzu babu bayani kan ko gobarar ta shafi na'urorin ko kuwa, kuma sannan hukumomi ba su yi karin haske ga makomar zaben kananan hukumomin jihar ba.

Labarai masu alaka