Shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da kisan mutum 19 a Benue

Shugaba Buhari ya sha alwashin zakulo maharan da kuma hukunta su Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Buhari ya sha alwashin zakulo maharan da kuma hukunta su

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan masu ibada 19 a wata coci da ke jihar Benue a tsakiyar Najeriya.

Wata sanarwa da kakakin gwamnatin Femi Adesina ya fitar ta ce, Shugaba Buhari ya sha alwashin zakulo maharan da kuma hukunta su.

Shugaban ya ce kisan mutanen a coci "aikin shaidanci ne,kuma yunkuri ne na haddasa rikicin addini, da janyo mummunan zubar da jini."

A nata bangaren gwamnatin jihar ta Benue ta yi kira ga hukumomi da su aika karin jami'an tsaro jihar, da nufin kawo karshen hare-haren da ake zargin makiyaya na kaiwa.

Babban daraktan yada labaran gwamnan jihar, Tahav Agerzua ya ce adadin mutanen da aka kashe yayin harin na safiyar Talata ya karu zuwa masu ibada 19 ciki har da limaman coci biyu.

An kai hari ne wata cocin darikar katolika watau St Ignatius Catholic Church a jihar Benue kamar yadda gwamnatin jihar ta bayyana.

Wasu mahara ne wadanda gwamnatin jihar ta ce makiyaya ne suka kaddamar da harin a garin Ayar-Mbalom da ke karamar hukumar Gwer ta Gabas.

Har ila yau maharan sun kona akalla gidaje kimanin 50, a cewar gwamnatin jihar.

Jihar Benue jihar ta dade tana fama da rikicin makiyaya da manoma.

Labarai masu alaka