Hukumar alhazai ta Najeriya ba zata bar mai zazzabin Lassa ba ya tafi aikin Hajj

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Miliyoyin Musulmai ne ke aikin Hajji a kowace shekara

Hukumar alhazai ta Najeriya ta ce kasar ta kawar da duk wata fargaba da hukumomin Saudiyya ke da ita game da batun zazzabin Lassa a Najeriya.

Ta kuma ce sun bullo da wasu matakan kariya tun kafin lokacin aikin hajjin bana, don gudun bacin rana.

Rahotanni a baya-bayan nan sun bayyana fargabar hana 'yan Najeriya zuwa kasa mai tsarki don sauke farali a bana saboda zazzabin Lassa da ake samu a wasu sassan kasar.

Shugaban hukumar Barister Abdullahi Muktar ya shaida wa BBC cewa za'a dauki matakai na ganin an hana duk wani maniyyaci daya nuna alamun kamuwa da cutar yadawa ga sauran maniyyata.

A shekarun baya dai 'yan Najeriya na mutuwa a kasar Saudiyya sakamakon kamuwa da cututtuka da kuma hadurra iri daban-daban.

Labarai masu alaka