Anya Buhari zai amsa gayyatar Majalisa kan rikicin Benue?

Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto JUSTIN TALLIS
Image caption An zabi Muhammadu Buhari ne bisa alkawarin samar da tsaro da yaki da cin hanci da rashawa

Majalisar wakilan Najeriya ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana a gabanta domin ya yi bayani kan yawan kashe-kashen jama'ar da ake yi a fadin kasar.

Daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu a tashe-tashen hankula a bana tsakanin manoma da makiyaya a sassan kasar da dama.

Ko a ranar Talata an kashe mutum 16 ciki har da wasu limaman coci guda biyu bayan da aka kai wa majami'arsu hari.

Rikicin na Benue da ma wasu sassan kasar, na kara matsa lamba kan Shugaba Buhari a daidai lokacin da zabe ke kara karatowa.

Kawo yanzu ba a bayyana lokaci ko ranar da shugaban zai bayyana ba.

Kudurin da aka gabatar a majalisar ya nemi Shugaba Buhari ya bayyana domin tattauna wa kan kashe-kashen na Benue da ma sauran yankunan kasar.

Babu wani martani ya zuwa yanzu daga fadar gwamnatin kasar kan wannan sammaci.

Wasu 'yan kasar da dama dai na nuna rashin gamsuwarsu kan yadda gwamnatin ke tunkarar batun rikice-rikicen.

Sai dai gwamnatin ta Shugaba Buhari, wanda aka zaba saboda alkawarin samar da tsaro, ta nace cewa tana daukar matakan da su ka dace domin shawo kan lamarin.

Amma kuma a zaman da 'yan majalisar wakilan kasar suka yi sun kada kuriar yanke kauna akan hafsoshin sojin kasar kuma sun nemi a ciresu daga mukamansu ba tare da bata lokaci ba.

'Yan majalisar sun dauki wannan mataki ne bayan da Hon Mark Gbilah da ke wakiltar Benue ya gabatar da wani kuduri a kan hari da sojojin suka kai a garin Naka da ke karamar hukumar Gwer ta yamma.

Rikicin manoma da makiyaya

Hakkin mallakar hoto AFP

Rikicin manoma da makiyaya dai a Najeriya ya yi sanadin asarar rayuka daga dukkan bangarorin biyu, al'amarin da ya jawo hankalin kusan daukacin 'yan Najeriya.

Rikicin ya fi kamari ne a jihohin Filato da Benue da Taraba da Nassarawa da Kaduna.

A baya gwamnatin tarayya ta yi kira ga gwamnonin jihohin da lamarin ya shafa su samar da wuraren kiwo.

Sai dai gwamnonin sun yi fatali da wannan kira, suna masu cewa ba su da isassun filayen da za su bayar domin kiwo.

Amma a watan Fabrairu Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya gayyaci Fulani makiyaya su koma jiharsa domin gudanar da kiyo ba tare da samun matsala ba.

Bayani kan ShugabaBuhari a takaice:

Hakkin mallakar hoto Photoshot
Image caption Wata mai goyon bayan Buhari na sumbatar hotonsa da aka manna
  • Shekararsa 75
  • An zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 28 ga Maris 2015
  • Ya yi shugaban mulkin sojan Najeriya daga 1984 zuwa 1985
  • An hambare shi a juyin mulki
  • Ya samu shaidar rashin kare hakkin dan adam
  • An yi amanna ba shi da cin hanci da rashawa
  • Mai ladabtarwa ne - a kan sa ma'aikatan gwamnati tsallen kwado idan suka yi lattin zuwa aiki
  • Musulmi ne daga arewacin Najeriya
  • Ya tsallake rijiya da baya a wani hari da Boko Haram ta kai masa