Arsenal ta baras da babbar dama - Arsene Wenger

Alexandre Lacazette Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Alexandre Lacazette ya ci wa Arsenal kwallonta

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce kulob din ya baras da babbar dama bayan da suka tashi kunnen doki 1-1 da Atletico Madrid.

Arsenal ce ta fara cin kwallo ta hanun Alexandre Lacazette a wasan dab da karshe na gasar cin kofin Europa a filin wasa na Emirates.

Amma Atletico ta rama ta hannun Antoine Griezmann ana dab da tashi duk da cewa an ba su jan kati tun minti 10 da fara wasan.

Wenger ya shaida wa gidan talbijin na BT Sport cewa: "Ganin irin wasan da muka taka da yadda wasan ya kasance, wannan mummunan sakamako ne, amma dole mu je gidansu da kwarin gwuiwa a wasa na biyu".

Wenger ya ce sun barar da wata babbar dama, yana mai cewa, "ya kamata a ce mun yi musu ruwan kwallaye amma hakan bai samu ba."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Antoine Griezmann ne ya rama wa Atletico kwallon da Lacazette ya fara ci.

Ya kara da cewa golansu ya kade kwallaye da dama sannan sun nuna kwarewarsu inda suka zira kwallo da damar da suka samu kwaya daya tal.

"Abu mai muhimmanci yanzu shi ne mu tunkari wasa na biyu da zummar cewa za mu iya doke su".

A ranar Alhamis ne Arsenal za ta ziyarci Metropolitano a Madrid domin fafatawa a wasa na biyu da Atletico, inda duk wanda ya samu nasara zai kai wasan karshe.

Sai dai kuma idan an tashi a haka zai kasance an fitar da Arsenal daga gasar.

Ana ganin wannan wata dama ce ga Arsene Wenger ya lashe kofi a kakarsa ta karshe a Arsenal, kuma lashe kofin zai ba kulob din damar zuwa gasar zakarun Turai ta badi.

Labarai masu alaka