Ana ce-ce-ku-ce kan nuna mata 'yan kokawa a Saudiyya

'Yan kokawara Turawa a Saudiyya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana son kokawar Turawa a Gabas ta Tsakiya

Gwamnatin Saudiyya ta nemi gafara bayan da wani hoton bidiyon mata 'yan kokawar Turawa ya yi kutse a yayin da jama'a ke kallon na Maza.

An gudanar da damben kokawar na (WWE) a birnin Jiddah, kuma maza da mata ne suka shiga kallo wanda kafar telebijin din kasar ta nuna kai tsaye.

Maza zalla ne suka fafata a kokawar a Saudiya yayin da aka haramta damben mata a kasar.

Amma mutanen Saudiya suna cikin tsakar kallo ne, sai ga tallar damben mata suna gani sanye da sigar tufafinsu.

Hoton ya fito a babban majigin da mutane ke kallo a dandalin da ake damben a filin wasanni na King Abdullah.

Wannan ne ya sa hukumar shirya wasanni ta Saudiya ta fito ta nemi gafara kan abin da ta bayyana a matsayin "abin da ba ya da kyau."

Kokawar dai wani sabon abu ne ga kasa kamar Saudiyya.

Amma wannan na daga cikin sabon salon hukumomin kasar na shigo da wasu nau'in nishadi ga jama'a domin samun kudaden shiga.

Kimanin mutane 60,000 ne suka shiga gidan kallon damben da suka kunshi mata da dama, wadanda tun tuni aka amince su shiga kallon wasannin kwallon kafa a shekarar nan a karon farko.

Tun da farko dai wasu sun soki gwamnatin Saudiyya na hana wa mata shiga damben na Wrestling da nufin kiyaye tsari da al'adun kasar.

Ana matukar son kokawar a yankin Gabas ta Tsakiya, Akwai shafin intanet na WWE da Larabci, kuma kamfanin ya sha shirya gasa a sauran kasashen da ke yankin.

A yanzu damben kuma ya shigo Saudiyya daga cikin sabbin manufofin Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman.

Labarai masu alaka